Chadi ta rufe kan iyakarta da Sudan har sai abin da hali ya yi
Chadi ta ce matakin ya biyo bayan kutse da kuma ƙeta iyaka da dakarun dake rikicin Sudan ke mata ne.
Gwamnatin Chadi ta bayyana ranar Litinin cewa ta rufe kan iyakarta da Sudan har sai baba ta gani, biyo bayan wasu jerin arangama tsakanin sojojin Chadi da ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke cikin yaƙin basasar Sudan a kan iyakar.
“Matakin ya biyo bayan kutse da keta iyaka da dakarun da suke rikici a Sudan suka yi ta yi ne a cikin ƙasar Chadi,” in ji Ministan Sadarwa, Mahamat Gassim Cherif a wata sanarwar da ya fitar, yana mai cewa yana son ya dakatar da “kowace barazanar yaɗuwar rikicin” zuwa ƙasarsa.
Rundunar RSF ta shafe kusan shekaru uku tana yaƙi da dakarun gwamnati a wani rikicin da ya kashe dubban mutane da kuma tilasta wa mutum miliyan 11 su tsere daga gidajensu, lamarin da ya tayar da abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ɗaya ne daga cikin rikicin jinƙai da ya fi tsanani.
Dakarun RSF sun ƙaddamar da wasu hare-hare kusa da kan iyakar Chadi, kuma aƙalla sojojin Chadi tara ne aka kashe a hare-hare daban-daban tun watan Disamba.
Sanarwar ranar Litinin ta ce Chadi “na da ‘yancin ramawa kan kowane harin tsokana ko kuma keta ‘yancin kan iyakarta”.
“An dakatar da kai komon kayayyaki da mutane,” in ji sanarwar, tana mai cewa za a iya yin rangwame saboda dalilai na jinƙai.