Kotun Najeriya ta tuhumi tsohon ministan shari'a Malami da laifukan ta'addanci
Masu shigar da ƙara sun yi zargin cewa Abubakar Malami "ya san" cewa yana "taimakawa wajen ɗaukar nauyin ta'addanci, ta hanyar ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta'addanci wadanda aka kawo batunsu ofishinsa".
Wata kotu a Najeriya ta tuhumi tsohon ministan shari'a Abubakar Malami da laifin ta'addanci, wanda kuma ke fuskantar zarge-zargen laifukan kuɗi.
Da farko an tuhumi Malami, wanda ya kasance babban lauyan gwamnati kuma ministan shari'a tsakanin Nuwamban 2015 zuwa Mayun 2023, tare da matarsa da ɗansa da laifin halatta kuɗaɗen haram da suka kai Naira biliyan 8.7 (kimanin dala miliyan 6).
Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta tuhume shi da "sanin" taimakawa wajen ɗaukar nauyin “ta'addanci, ta hanyar ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta'addanci wadanda aka kawo batunsu ofishinka".
An tuhumi Malami tare da ɗansa Abdulaziz Malami da laifin "yin aikin ta'addanci ta hanyar mallakar bindiga da harsasai marasa lasisi a gidansa."
Dukansu sun musanta laifukan.
Nijeriya ta shafe shekaru goma sha biyar tana yaƙi da masu ɗauke da makamai, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da korar wasu kusan miliyan biyu daga gidajensu.
An ba da belin Malami a watan da ya gabata a shari'ar halatta kudaden haram, amma an sake kama shi jim kaɗan bayan an sake shi.
Malami shi ne babban jami'in gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya fuskanci shari'a bisa zargin zamba.