Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra’ila bayan Trump ya yi iƙirarin daƙile ƙarfin sojinta

Ƙararrawar gargadin hare-haren sama ta rika yin kara a sassa da dama na arewacin Isra’ila, a cewar gidan talabijin na Channel 12.

By
Iran ta kai miyagun hare-hare na makamai masu linzami a Tel Aviv don mayar da martani kan sabbin hare-haren Amurka da Isra'ila a Isfahan / AA

Rahotanni daga tashar ta Channel 12 ta Isra’ila sun bayyana cewa Iran ta harba manyan jerin makamai masu linzami har guda uku zuwa arewacin Isra’ila tun da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Ƙararrawar gargaɗi hari ta sama ta riƙa kaɗawa a sassan arewacin Isra’ila yayin da tashar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kakkaɓo makaman daga sararin samaniya.

Gidan talbijin na gwamnatin Iran ya yi iƙirarin cewa makaman sun isa birnin Haifa mintoci kaɗan bayan kalaman Shugaba Trump na cewa yanzu Iran ba ta na’urorin harba makamai masu yawa.

Tun da farko a ranar Alhamis, a wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin daga Fadar White House, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran tana da “ƙalilan” ɗin na’urorin harba makamai da suka rage, inda ya ƙara da cewa ƙarfinta na harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi “an rage su sosai.”

Hakazalika, Trump ya shaida wa ’yan Amurka cewa yana ganin yaƙin da ake yi da Iran zai ci gaba har zuwa tsawon makonni biyu zuwa uku, amma ya bayyana yaƙinin cewa rikicin yana gab da zuwa ƙarshe.

Yankin dai yana cikin hali na fargaba tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da harin ta sama a ranar 28 ga watan Fabrairu, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,340, ciki har da Jagoran Addini na ƙasar, Ali Khamenei.

Ita ma Iran ta mayar da martani ta hanyar amfani da jiragen marasa matuƙa da makamai masu linzami kan Isra’ila, tare da Jordan, Iraƙi, da kuma ƙasashen Larabawa da ke sansanonin sojin Amurka, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da lalata ababen more rayuwa, sannan ya dagula harkokin kasuwannin duniya da zirga-zirgar jiragen sama.