| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin NATO don tattaunawa kan yara, fasaha da tsaro
Maidakin Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashe mambobin NATO da suka zo Ankara don halartar taron NATO karo na 26 a fadar Cankaya.
Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin NATO don tattaunawa kan yara, fasaha da tsaro
Maidakin Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin NATO a Ankara a ranar 8 ga Yulin 2026. / َAA

Maidakin Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashe mambobin NATO a wani zaman tattaunawa mai taken “Yara, Fasahar Kere-Kere da Tsaro: Kare Al’ummu Masu Zuwa” a wani bangare na taron NATO a ranar 8 ga Yuni.

Erdogan ta gana da matan dukkan shugabannin da suka halarci zaman a lokacin da suka isa Fadar Cankaya.

Brigitte Macron, matar Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron, ta ce Faransa na kokarin takaita amfani da na’urorin kwamfuta da dangoginsu a makarantu.

Macron ta ce “Misali, abinda ka karanta a kwamfuta bas hi da tairi irin na wand aka karanta a littafi. Me ya sa muke takaita wadannan? Saboda mun gano wasu abubuwa. Saboda wadannan ba irin koyarwar da aka saba a ita ba ce. Ba ma son yara su saba da wadannan abubuwa tun suna kanana.”

Macron ta lura da cewa yara na kallon bidiyon yaudara da za su iya yaudarar kowa, tana mai kara wa da cewa “Muna bukatar kare duniyar gobe a yau. Matsalar tamu ce. Muna kallon yadda take gudana. Akwai bukatar mu magance ta.

Da take tabo batun amfani da Kirkirarriyar Basira, Macron ta ce a Faransa ana fada wa dalibai su kula sosai wajen zabin aikin da za su yi, tana mai cewa “Muna fada musu da su zabi sana’ao’I a nutse. Akwai cigaba cikin hanzari. Akwai damuwa. Ba mu san har zuwa ina lamarin zai kai ba.”

Diana Nausediene, maidakin shugaban kasar Lithuania, ta bayyana cewa kowa ya yarda cewa dole ne duniyar yanar gizo ta zama mai tsaro ga yara, tana mai kara wa da cewa dole a kare yara kanana daga cin zarafi ta yanar gizo, bayanan karya da yi musu ta fuska biyu.

Nausediene ta jaddada cewa dole ne masu tsara manufofi su yi aiki tare da al’umma, tana mai cewa “muna fuskantar babban kalubale, kuma muna bukatar kokarin kasa da kasa.”

Da take kiran kawayen NATO da su hada kai waje guda don kare matasa daga cutuwa ta fuska biyu, Nausediene ta bayyana cewa matasa masu karancin shekaru ne “mafiya rauni wajen samun bayanan karya.”

Maidakin shugaban kasar Finland, Suzanne Innes-Stubb ta bayyana cewa duniyar yanar gizo na bayar da amfani sosai kuma matasa na amfani da shafukan sada zumunta don zama tare, kulla mu’amala, koyo da samun bayanai.

Innes-Stubb ta ja hankali kan hatsarin da ke tattare da yada bayanan karya, tana mai cewa a wajen yara da yawa, duniyar yanar gizo wani bangare ne na rayuwar yau da kullum, kuma yara da yawa na shigowa duniyar a kowacce dakika.

Rumbun Labarai
Turkiyya da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa kan ƙera jiragen ruwa
Shugaba Erdogan ya taya tawagar Sultans of Net ta Turkiyya murnar lashe gasar ƙwallon raga ta mata
Shugaba Erdogan ya yi taron cika shekaru shida da sake bude Hagia Sophia don Ibadar Musulmai
Ayyukan ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila na barazana ga ƙoƙarin zaman lafiya a Ƙudus: Turkiyya
Turkiyya ta yi kira ga Amurka da Iran su koma kan yarjejeniya, su kuma yi aiki tare da Qatar
Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5 ta auka wa gabashin Turkiyya
Ga yadda Turkiyya ke son hana ‘yan ƙasa da shekaru 18 shan taba sigari
Dangantakar Turkiyya da Afirka da yaƙi da FETÖ bayan yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli da aka daƙile
Matar shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta tuna da ranar murƙushe yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli
Daƙile yunƙurin juyin mulki na 2016 ya 'bayyana 'yancin kai' na ƙarni ga Turkiyya, in ji  Erdogan
Turkiyya na juyayin cika shekaru 10 da yunƙurin juyin mulki na ranar 15 ga Yuli da bai yi nasara ba
Turkiyya ta umarci makarantu su goge hotunan ɗaliban da aka wallafa ba tare da izinin iyaye ba
Jami’an leƙen asiri na Turkiyya sun kama wani babban jami’in Daesh a Syria
Manufofi da gwamnatin Netanyahu 'nauyi' ne ga Isra'ila da yankin da tsaron duniya: Ministan Turkiyya
Shugaba Erdogan ya ce taron NATO a Ankara ‘nasara ce ta tarihi’
Taron Trump-Erdogan: Amurka za ta ɗage wa Turkiyya takunkumai, za a yanke hukunci kan F-35 nan kusa
Tsaron Turai ba zai ta’allaka ga Tarayyar Turai ba, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan
Taron Koli na NATO a Ankara na nuna muhimmiyar rawar Turkiyya a harkar tsaro da diflomasiyyar duniya
Muhimmin labarin fursunonin yaki Turkawa da ya sauya fasalin aƙidun horon sojojin NATO
Turai za ta yi amfani da taron NATO a Ankara ta nuna wa Trump kyakkyawar niyyarta kan tsaro: Jamus