| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da fiye da mutum 400 a kotu a Abuja kan zarginsu da ta'addanci
Ana gurfanar da wadanda ake zargin cikin rukuni-rukuni a dakunan kotun daban-daban inda aka dakatar da shari'o'i da dama don ba wa alkalai damar sauraron shari'ar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da fiye da mutum 400 a kotu a Abuja kan zarginsu da ta'addanci
Wadanda ake zargin suna fuskantar tuhume-tuhumen ta'addanci, ba da tallafi na kudi ga ta'addanci, da kuma taimakawa / TRT Afrika Hausa

Gwamnatin Nijeriya a ranar Litinin ta gurfanar da fiye da mutane 400 da ake zargi da aikata ayyukan ta'addanci a gaban alkalan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Ana gurfanar da wadanda ake zargin cikin rukuni-rukuni a dakunan kotun daban-daban inda aka dakatar da shari'o'i da dama don ba wa alkalai damar sauraron shari'ar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, ne ke jagorantar tawagar masu gabatar da kara, tare da goyon bayan Daraktan Lauyoyin gwamnatin Tarayya, Rotimi Oyedepo, wadanda dukkansu biyu manyan Lauyoyi ne na Nijeriya rike da mukamai na SANs.

Cibiyar ba da taimako kan shari’o’i a Nijeriya ce take wakiltar wadanda ake tuhuma marasa galihu.

Wadanda ake zargin suna fuskantar tuhume-tuhumen ta'addanci, ba da tallafi na kudi ga ta'addanci, da kuma taimakawa da kuma tallafa wa ayyukan ta'addanci.

Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayya, John Tsoho, ya nada wasu alkalan kotun don zaman sauraron kararrakin na musamman.

An taɓa irin wannan shari’a ta bai ɗaya a watan Afrilun 2026.

A watan Afrilun 2026 an gudanar da irin wannan zaman shari’a na bai ɗaya a kotun a watan Afrilu, inda Gwamnatin Tarayya ta ce ta yanke wa mutane 386 hukunci kan laifukan ta'addanci.

Daga cikin mutane 508 da ake tuhumarsu a shari’ar, ofishin Antoni Janar ɗin ya yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutane 386, tare da sallamar mutane 8 da kuma wanke mutum 2 daga tuhuma.

Mafi yawa daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, an same su da laifin alaka da ayyukan ta’addanci, kamar taimakawa da sanya kudadensu a ciki, sun kuma fuskanci hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Shari'o'in na bai ɗaya sun bayyana yadda gwamnatin Nijeriya ke kokarin hanzarta shari'o'in ta'addanci da aka jinkirta, inda a yanzu ake gudanar da shari'o'i a Abuja maimakon sansanin sojoji da ke Kainji na Jihar Neja.

Rumbun Labarai
'Yansandan Nijeriya sun kama Adeniyi wanda ake zargi da kafa hukumar bogi
Nijeriya da Masar na shirin karfafa hadin gwiwa a yaki da miyagun kwayoyi
Matsalar ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi tsakanin mata a Nijeriya
Matatar Dangote ta koma amfani da farashin dala don sayar da manta maimakon naira
'Yanbindiga sun kashe mutane aƙalla 18 a Jihar Benue da ke tsakiyar Nijeriya, in ji mazauna yankin
Abin da zuwan kasuwar hannun-jarin Nijeriya ta farko a duniya ke nufi
Ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai matakin da ya fi yawa tun watan Yunin 2020
Sojojin Nijeriya sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP da gano wasu Larabawa masu horas da ‘yanta'adda
NDLEA ta kama 'yar Afirka ta Kudu kan zargin amfani da ɗanta mai shekara 3 wajen safarar hodar iblis
Hare-haren saman sojin Nijeriya sun kashe gomman 'yanta'addan Boko Haram
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda' fiye da 300 a Zamfara
Jami'an tsaron Nijeriya sun ceto daliban da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo
Nijeriya ta zo ta farko a duniya a tagomashin kasuwar hannun-jari
Wasu da ake zargi ’yan ISWAP ne da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya
Matatar mai ta Dangote ta fara dakon fetur kyauta zuwa wasu jihohin Nijeriya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Jihar Legas ta kama mabarata 396, tana tantance bayanansu domin mayar da su jihohinsu na asali
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Gwamnatin Nijeriya ta bai wa 'yan ƙasarta damar ƙarshe ta kwashe su daga Afirka ta Kudu
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto