Mayaƙan RSF sun kai hari a Jami'ar Kordofan
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun ce hari kan wuraren ba da ilimi ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Jami’ar Kordofan ta Sudan ta ce reshenta dakarun RSF sun kai hari da jirage marasa matuƙa a reshenta da ke birnin El-Obeid inda suka lalalata abubuwa da yawa ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa, ofishin watsa labaran jami’ar ya ce an kai harin ne a gine-ginen da ke tsakiyar reshen jami’ar a El-Obeid, babban birnin jihar North Kordofan, lamarin da ya janyo “lalacewa mai yawa” ga ababen more rayuwa.
Ba a ba da bayanai kai-tsaye ba game da adadin mace-mace a hare-haren ba.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama da ƙasar, Emergency Lawyers Association, ta yi tir da hare-haren kuma ta ɗora alhakinsa kan RSF, tana mai bayyanasu a matsayin wani ɓangare na ƙarin hare-haren da ake yi kan wuraren fararen-hula.
Kai hare-hare kan makarantu “keta dokokin ƙasa da ƙasa ne,” in ji ƙungiyar, tana mai jaddada cewa hare-hare kan jami’o’i na zagon ƙasa ga ‘yancin neman ilimi tare da barazana ga makomar ɗalibai.
Yaƙin basasa ya ɓarke tsakanin sojin ƙasar Sudan da rundunar RSF tun watan Afrilun shekarar 2023, inda aka kashe dubban mutane, da kuma raba kimanin mutane miliyan 13 da gidajensu, da kuma haddasa ɗaya daga cikin matsaloli na jinƙai da suka fi muni a duniya, in ji rahotannin Majalisar Ɗinkin Duniya.