| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Dakarun Iran sun ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa kan jiragen ruwan Amurka bayan wani jirgin ruwan yaƙin Amurka ya buɗe wuta da kuma ƙwace wani jirgin ruwa na dako mai tutar Iran, in ji kamfanin dillancin labaran Tasnim.
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Mai magana da yawun sojin Iran Ebrahim Zolfaghari ya ce dakarun Amurka sun buɗa wuta kan jirgin ruwan kafin su shige shi. / Reuters

Dakarun Iran sun ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa ranar Lahadi a kan jiragen ruwan Amurka a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren da dakarun Amurka suka kai kan wani jirgin ruwan tare da ƙwace shi, in ji kafafan watsa labaran ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda ƙasar ke da ƙwarya-ƙwaryar iko a kansa ya ruwaito cewa dakarun Amurka sun shiga jirgin mai dakon kaya na kwantena mai suna TOUSKA a gaɓar Tekun Oman, kuma Iran ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa kan jiragen ruwan Amurka, ba tare da bayyana cewa jiragen da aka kai wa harin na soji ba ne ko na ‘yankasuwa ba.

Iran ta tabbatar daga farko cewa dakarun Amurka sun ƙwace jirgin ruwan Iran ɗin kuma ta yi gargaɗin cewa za ta ɗau fansa “ba da jimawa ba” bayan matakin, wanda ta kira keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu da Pakistan ta taimaka wajen ƙullawa wadda ta yi aiki a mafi yawan lokuta tun lokacin da aka ayyana ta ranar 7 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labaran Fars, wanda shi ma ƙasar na da ƙwarya-ƙwaryar iko a kansa, ya ba da rahoton cewa hedikwatar rundur Khatam al-Anbiya ta ce dakarun Amurka sun kai hari kan jirgin ruwan, sun lalata na’urar gane hanyarta kana suka shige shi bayan abin da ya bayyana a matsayin saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Bayanai na bibiyar jiragen ruwa sun nuna cewa jirgin TOUSKA ya bar tashar jiragen ruwa ta Port Klang a Malaysia ranar 12 ga watan Afrilu ne.

Mai magana da yawun sojin Iran Ebrahim Zolfaghari ya ce dakarun Amurka sun buɗa wuta kan jirgin ruwan kafin su shige shi.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya fara bayar da sanarwar aukuwar lamarin ranar Lahadi kuma daga baya hedikwatar runduna ta tsakiya ta Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da shi, inda ta ce jirgin yaƙi USS Spruance ne ya tare jirgin ruwa na dakon kaya ɗauke da tutar Iran, wanda ya yi ƙoƙarin karya ƙawanyar sojin ruwan Amurka a Tekun Oman.

Hedikwatar rundunar ta CENTCOM ta ce sojojin ruwan sun ci gaba da riƙe jirgin a hannun Amurka. Ya bayyana a wata sanarwa cewa jirgin na kan hayarsa ta zuwa tashar jirgin ruwan Iran ta Bandar Abbas ne lokacin da lamarin ya auku.

CENTCOM ya kuma fitar da wani bidiyo a shafin sada zumunta na Amurka X, inda ya nuna wani jirgin yaƙin ruwa na Amurka yana ba da gargaɗi kafin ya yi harbi kan jirgin.

“Amurka mai tsangwama, da saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma aiwatar da fashin teku, ta kai hari kan ɗaya daga cikin jiragen ruwan Iran bayan ta lalata tsarin gane hanayarsa” in ji Zolfaghari.

Ya ƙara da cewa dakarun Amurka US sun shiga jirgin ruwan bayan sun tura “wasu ‘yanta’adda sojin ruwa” cikinsa.

“Muna gargaɗin cewa dakarun sojin Iran za su mayar da martani ba da jimawa ba kuma za su ɗau fansa kan wannan aikin fashin teku da makamin da sojin Amurka ta yi,” in ji shi.

MAJIYA:TRT World