Umrah 2026: Rufe filin jirgin saman Dubai ya tsayar da sufurin masu zuwa Umrah daga Nijar

Dakatar da ayyuka a wannan filin jirgin, wanda mafi yawan jiragen maniyyatan Nijar ke bi ta cikinsa don zuwa Saudiyya, ya dagula lissafin kamfanonin sufuri har ma da Hukumar Shirya Aikin Hajji da Umrah ta kasar Nijar (COHO).

By
Umrah / Reuters


Aikin jigilar maniyyatan Nijar zuwa Saudiyya don gudanar da Umrah a watan Ramadan ya fuskanci cikas tun bayan rufe filin jirgin saman Dubai a karshen makon jiya saboda hare-hare jirage marasa matuka da Iran take kai wa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sakamakon yakin da Amurka da Isra’ila suke yi da Iran.

Dakatar da ayyuka a wannan filin jirgin, wanda mafi yawan jiragen maniyyatan Nijar ke bi ta cikinsa don zuwa Saudiyya, ya dagula lissafin kamfanonin sufuri har ma da Hukumar Shirya Aikin Hajji da Umrah ta kasar Nijar (COHO), kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Nijar (ANP) ya bayyana.

“Rufe filin jirgin saman Dubai shi ne kawai matsalar da ta jawo cikas game da sufurin maniyyatan. Dukkan maniyyatan da jiragensu ya kamata su bi ta Dubai an soke tafiyarsu.

“Su kuwa waɗanda suka riga suka isa Saudiyya, a hanyarsu ta dawowa ne za su iya fuskantar cikas,” in ji Guibrima Ali Boukar, shugaban sashin sadarwa na Hukumar COHO, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na ANP.

Ya ƙara da cewa: “Akwai rukunin maniyyata da aka soke jirginsu. Kamfanonin jigilar da suka yi rijista da su suna ƙoƙarin yin shatar wasu jiragen musamman da aka shirya za su tashi a ranar Lahadi, 8 ga Maris, 2026.

A gefe guda kuma, wasu maniyyatan sun fasa tafiya saboda fargabar rikicin da ke faruwa a yankin Gabas Ta Tsakiya.”

A cewar Elhadj Karimou Moustapha, ɗaya daga cikin manajojin kamfanin jigilar na Bab Al Sabour: “Kafin fara wannan rikici, mun sami damar jigilar kusan mutane hamsin a rukuni daban-daban.

“Gaba ɗaya za mu iya ƙiyasta adadin maniyyatan Nijar da aka riga aka kai ƙasa mai tsarki sun wuce mutum 500.”

Sakamakon dakatar da ayyuka a filin jirgin saman na Hadaddiyar Daular Larabawa, kamfanin Bab Al Sabour yana binciken wata hanyar daban.

“A daren nan (Litinin, 9 ga Maris, 2026), muna da mutane 32 da za mu kwashe idan an tabbatar da jirgin,” in ji Elhadj Karimou. Waɗannan jiragen na musamman ne da aka nema waɗanda za su tashi kai tsaye daga Niamey zuwa Madina.

“Akwai wasu batutuwa na sufuri da ba zan iya yin tsokaci a kansu ba, amma abin da yake tabbas shi ne rufe filin jirgin saman Dubai biyo bayan hare-hare na ci gaba da kawo cikas ga ayyukanmu na jigilar maniyyata,” in ji shi.

“Ya kuma nuna damuwarsa ga maniyyatan da aka tsara za su dawo ta Dubai idan yanayin bai inganta ba.

Filin jirgin saman Dubai (DXB) ya dakatar da ayyukansa na ɗan lokaci a ranar Asabar, 7 ga Maris, 2026, bayan kakkabo wasu makamai masu linzami da jiragen marasa matuka da suka janyo babban cikas.

Iran ce ta harba waɗannan makaman tana nufin sansanonin sojin Amurka da ke UAE (ciki har da birnin Dubai), a matsayin martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila suka kai mata a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Rahotanni sun nuna cewa ayyukan filin jirgin suna dawowa sannu a hankali, amma zirga-zirga jirage ba dawo ba yadda take a baya ba, akwai soke-soke da rashin tabbas na jadawalin tashi saboda yanayin tsaro.

Har ila yau, a cikin wannan rikici na Amurka da kawayenta Isra’ila da Iran, kasar Iran ta kuma kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke Saudiyya, lamarin da ya zama abin damuwa ga maniyyatan Nijar da kamfanonin sufuri.

Wani jami’in diflomasiyyar Nijar da ke Jeddah mai suna Mahaman ya tabbatar da cewa harin da Iran ta kai kan yankin Saudiyya bai shafi wuraren ibada ba.

“Wuraren ibada ba su fuskanci wani hari ba, haka ma birnin Jeddah. Abin da mutane ke faɗa gaskiya ya samo asali ne saboda yadda wasu kafafen yada labarai suke kara zuzuta abin,” in ji jami’in.

Wata maniyyaciyar Nijar, wacce ta isa Saudiyya a farkon watan Ramadan kafin fara rikicin, ta tabbatar da hakan.

“A dukkan wuraren ibada, mutane suna gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali. Ni ma ban sani ba ko an kai hari; sai da mutane suka kira ni daga Nijar suka sanar da ni. Hakika, akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a nan,” in ji ta.

A nan Niamey, ita ma hukumar COHO ta bayyana irin wannan saƙon.

“A Saudiyya, rahotannin da muke samu sun nuna cewa maniyyata suna cikin koshin lafiya. Suna gudanar da ibadarsu ba tare da wata matsala ba,” in ji Guibrima daga sashin sadarwa na hukumar COHO.

“Idan filin jirgin saman Dubai ya kasance a rufe har zuwa ƙarshen Ramadan, za mu yi la’akari da yin aiki da wasu kamfanonin da ba sa bi ta can, kamar kamfanin Turkish Airlines, Royal Air Maroc, Air Algérie, ko kuma jiragen haya na musamman,” in ji jami’in na Nijar.