Hukumar NCDC ta Nijeriya ta tabbatar da samun mutum 318 ɗauke da zazzaɓin Lassa da mutuwar mutum 70
Babban Darakta kuma Shugaban Hukumar NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai a ranar Juma’a.
Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya, NCDC, ta tabbatar da samun mutane 318 da suka kamu da zazzaɓin Lassa da kuma mutuwar mutane 70 a fadin ƙasar tun daga farkon shekarar 2026.
Babban Darakta kuma Shugaban Hukumar NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai a ranar Juma’a.
Ya ce an samu Jumullar mutane 1,469 da ake zargi da kamuwa da cutar, lamarin da ya sa adadin waɗanda ke mutuwa daga cutar ya kai kashi 22 cikin 100.
A cewarsa, jihohi biyar waɗanda suka haɗa da Edo, Ondo, Taraba, Bauchi da Ebonyi ne ke ɗauke da kashi 91 cikin 100 na dukkan waɗanda aka tabbatar suna ɗauke da cutar. Haka kuma, ƙananan hukumomi goma ne ke da kashi 68 cikin 100 na kamuwa da cutar.
Domin daƙile ɓarkewar cutar, Idris ya ce NCDC ta tura Rundunar Gaggawa ta Kasa zuwa jihohi takwas da suka bayar da rahoton cutar.
Ya ƙara da cewa hukumar tana aiki tare da gwamnatocin jihohi domin ƙarfafa sa ido da kula da marasa lafiya, da kuma wayar da kan al’umma.
“Kare ma’aikatan lafiya na daga cikin manyan abubuwan da muka fi bai wa muhimmanci,” in ji Dakta Idris, inda ya nuna cewa ma’aikatan lafiya 15 sun kamu da cutar tun daga farkon shekarar nan. Ya ce rashin fahimtar hadari da kuma rashin kyakkyawan tsarin kare kamuwa da cutar a wasu cibiyoyin lafiya na daga cikin dalilan hakan.
NCDC ta bayyana wasu kalubale da ake fuskanta, ciki har da rashin bin diddigin waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar yadda ya kamata da jinkirin neman magani da kuma ƙarancin kuɗaɗen da jihohi ke warewa don ayyukan rigakafi, lamarin da ka iya ƙara yawan kamuwa da cutar da mace-mace.
Idris ya jaddada rawar da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen gano masu cutar da wuri da isar da saƙonnin gargaɗi ga al’umma, da kuma tsaurara aiwatar da matakan kariya da daƙile yaɗuwar cuta.
Har ila yau, ya yi gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya da jita-jita, kamar rahoton ɓarkewar cutar da ba gaskiya ba da aka yaɗa kwanan nan a sansanin Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC) na Jihar Kwara, wanda ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin daƙile cutar.
Idris ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kula da tsaftar muhalli, su adana abinci yadda ya dace, su dakile beraye, tare da gaggauta neman kulawar likita idan aka ga alamun cutar, domin rage yaduwar cutar Lassa.