Ghana da Zambia sun ƙulla yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba yayin ziyarar Mahama
Shugaba Mahama ya isa Lusaka ranar Laraba , 4 ga watan Fabrairu, inda aka karɓe shi hannu bibbiyu a filin jiragen saman Kenneth Kaunda na ƙasa da ƙasa, inda ya samu tarbar takwaransa na Zambia, Shugaba Hakainde Hichilema.
Ghana da Zambia sun ƙulla wata muhimmiyar yarjejeniya da ta bai wa ‘yan ƙasashen biyu damar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba.
Ministan harkokin wajen ƙasar Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ne ya bayyana haka a lokacin da Shugaba John Dramani Mahama ya fara ziyarar aiki ta kwana uku a Zambia, wadda ke da zummar ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu.
Shugaba Mahama ya isa Lusaka ranar Laraba , 4 ga watan Fabrairu, inda ya samu tarba ta musamman daga takwaransa na Zambia, Shugaba Hakainde Hichilema a filin jirgin saman Kenneth Kaunda na ƙasa da ƙasa.
Da yake jawabi ga manema labarai a lokacin ziyarar, Mista Ablakwa ya bayyana matakin ɗauke buƙatar bizar a matsayin mafi muhimmanci a dangantakar ƙasashen biyu.
Ya ce matakin zai sauƙaƙa tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasashen tare da buɗe sabbin damarmaki a harkokin cinikayya da yawon buɗe ido da zuba jari da kuma musayar al’adu.
“A matsayinmu na ma’aikata, muna ba da fifiko ga tafiye-tafiye na mutanenmu cikin sauƙi kuma ɗaya daga cikin muhimman sakamakon wannan ziyarar shi ne, a karon farko cikin tarihin dangantaka tsakanin Ghana da Zambia, za mu samu tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen biyu ba tare da buƙatar biza ba,” in ji shi.
“Ba za ka sake damuwa game da biza ba. Wannan matakin ɗauke bizar bayyanannen umarni ne daga Shugaba Mahama. Ya shaida mini ƙarara cewa idan ba a cim ma hakan ba, kada ma na shiga cikin tawagar ziyarar.”
Mista Ablakwa ya ƙara da cewa manufar tafiya babu biza ta cire daɗaɗɗen ƙalubale a hukumance da ‘yan Ghana da ‘yan Zambia ke fuskanta, ciki har da ɗalibai da ‘yankasuwa da masu yawon buɗa ido da ƙwararru kuma ana fatan inganta tafiya-tafiye da haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu.