| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Adadin mutanen da suka mutu a Congo saboda kamuwa da Ebola ya kai 131
Ɓarkewar cutar mai haɗari ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran ƙungiyoyi na duniya sun fitar da gargaɗi.
Adadin mutanen da suka mutu a Congo saboda kamuwa da Ebola ya kai 131
Kongo ta tsaurara binciken lafiya a iyakar Barrier bayan tabbatar da ɓullar cutar Ebola nau'in Bundibugyo a Goma. / Reuters

Ɓarkewar cutar Ebola mai saurin yaɗuwa ya kashe mutane aƙalla 131 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, in ji jami’an ƙasar ta tsakiyar Afirka, bayan sun sake sabunta adadin daga mutanen 118 da aka bayar a baya. Likitoci suna bibiyar sama da mutane 500 da ake zaton sun kamu da cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta gudanar da zaman kwamitin gaggawa a ranar Talata don tattauna wannan ɓarkewar cutar mai kisa.

"An shirya zaman kwamitin gaggawa nan gaba a yau," kamar yadda wani mai magana da yawun WHO ya shaida wa AFP, kwanaki biyu bayan shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana ɓarkewar cutar a matsayin wani babban bala’i ga kiwon lafiya a duniya.

Nau'in Ebola mai suna Bundibugyo, wanda ba a sab gani ba, ya sa WHO ta ayyana ɓarkewar a matsayi wani babban bala’i ga kiwon lafiya da ke ɗaga hankalin duniya baki ɗaya.

Mafi yawan waɗanda suka kamu suna Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kuma annobar ta yaɗu zuwa Uganda, inda aka fara gano wannan nau'in a shekarun 2007-2008.

Nau’in Bundibugyo na kashe kusan kashi 30 zuwa 40 cikin dari na waɗanda suka kamu, abin da ke nuna cewa ba shi da matuƙar haɗari kamar nau’in Zaire da aka fi sani, wanda bincike na duniya da aka buga a 2024 ya nuna na iya haifar da mutuwa har zuwa kashi 90 cikin dari.

Bundibugyo ɗaya ne daga cikin nau'ika hudu na rukunin ƙwayar Ebola da suke haifar da cuta mai barazana ga rayuwar mutane. Dukkan ƙwayoyin Ebola ana yaɗa su ne ta hanyar mu'amala kai tsaye da ruwan jikin dabbobi ko mutane masu ɗauke da cutar, ko ta abubuwa da suka gurɓata daga irin waɗannan ruwan.

Yaɗuwar ta hanyar ruwan jiki babban haɗari ne musamman ga ma'aikatan asibitoci. Wani likitan Amurka da ke aiki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya kamu a wannan ɓarkewar.

Babu allurar rigakafi ko magani da aka amince da su musamman don kwayar Bundibugyo. Za a buƙaci izinin amfani na gaggawa kafin a yi amfani da kowanne maganin gwaji ko magungunan da aka riga aka nuna sun yi tasiri kan wasu nau'ikan.

Wasu magungunan gwaji da suka taimaka wajen daƙile Bundibugyo a gwaje-gwajen da aka yi a kan dabbobi sun haɗa da Ervebo na Merck, MBP 134 na Mapp Biopharmaceutical, da VesiculoVax na Auro Vaccines.