Sojojin Nijar sun ce sun halaka ‘yan ta’adda 43 a yankin Diffa

“Ayyukan da sojojin ƙasa suka gudanar tare da goyon bayan hare-haren jiragen sama na hadin gwiwa, ya yi sanadin hallaka ‘yan ta’adda 43 da kama mutane 28 da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda,” in ji Cibiyar Hadin Gwiwar Ayyuka ta Sojojin Nijar.

By
Nijar na fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a yankuna da dama tun daga shekarar 2015. / AA

Sojojin Nijar sun bayyana cewa sun hallaka ‘yan ta’adda 43 tare da kama 28 ake zargi da kasancewa “da taimaka musu” a yayin wasu hare-haren haɗin gwiwa na ƙasa da sama da aka gudanar a wurare daban-daban na kasar.

“Ayyukan da sojojin ƙasa suka gudanar tare da goyon bayan hare-haren jiragen sama na hadin gwiwa, ya yi sanadin hallaka ‘yan ta’adda 43 da kama mutane 28 da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda,” in ji wata sanarwa daga Cibiyar Hadin Gwiwar Ayyuka ta Sojojin Nijar (CICO) da aka karanto a gidan talabijin na gwamnati a ranar Alhamis.

 “Waɗannan ayyuka sun kuma kai ga ƙwace makamai da harsasai masu yawa,” in ji majiyar, tana mai karin bayani cewa an kuma kwace kayayyaki daban-daban ciki har da nakiya dubu biyar da dari hudu da hamsin da biyu (5,452), da wayoyin tayar da nakiyoyin 68 da fiye da lita 68,000 na kayan fasa-ƙauri, da kuma dubban ƙwayoyi masu illa da aka shirya kai wa ƙungiyoyi masu aikata laifuka

Nijar na fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a yankuna da dama tun daga shekarar 2015.

Wannan ya haɗa da yankin Diffa mai iyaka da Nijeriya inda ƙungiyar Boko Haram ke aiki, da kuma yankunan Tahoua da ke arewa maso yamma da Dosso da ke kudu maso yamma da Tillabéri da ke yammacin ƙasar waɗanda ke fuskantar hare-haren da ake dangantawa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh.

Wannan kungiya ce ta dauki alhakin harin da aka kai a ranar 29 ga Janairu kan filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Diori Hamani da ke babban birnin Nijar, wato Yamai.