Wani helikwafta na asibiti ya yi hatsari a sansanin Al-Sarra na Libya yayin da yake dowowa daga aikin kuɓutar da mara lafiya, lamarin da ya kashe mutum biyar, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwaito.
Hatsarin da ya faru ne ranar Litinin, kimanin kilomita 300 (mil186) daga birnin Kufra da ke kudu maso gabashin ƙasar, kamar yadda kafar intanet ta al-Wasat ta ruwaito, inda ta ambato majiyoyin da suke da sani game da lamarin.
Waɗanda hatsarin ya kashe sun haɗa da mambobin rundunar sufuri ta soji biyu da kuma wani ma’aikacin jinya ɗaya daga Kufra.
Saura mutane biyun ‘yan ƙasar waje ne, waɗanda aka bayyana a matsayin mai tuƙa jirgi da mataimakinsa, in ji rahoton.
Ba a ƙara wani bayani ba nan take game da hatsarin, kuma hukumomin Libya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba tukunna game da lamarin.
Aikin kuɓutarwa
Kafar watsa labarai ta ƙasar mai suna Aviation Today ta ba da rahoton cewa helikwaftar na soji yana aikin kuɓutarwa ne bayan wani soja ya ji rauni a wani hatsari a yankin hamada mai nisa kusa da Kufra.
Jirgin na ɗauke da jami’an sifiri na soji biyu da jami’an jinya da ma masu tuƙin jirgin a lokacin da ya yi ƙasa kafin ta koma sansaninta.
Rahoton ya ƙara da cewa jami’an ba da taimakon gaggawa sun kai ga inda lamarin ya auku da wuri, amma ta tabbatar da cewa babu wanda ya tsira daga cikin waɗanda suke cikin jirgin.




















