| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz: Rahoto
Jami'an tsaron Rundunar juyin-juya-hali na Iran sun harba akalla makamai masu linzami biyu kan jiragen ruwan kasuwanci da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz.
Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz: Rahoto
Jirgin ruwan yana bakin mashigar ruwa, a Tekun Oman, lokacin da aka kai masa hari, in ji WSJ. / Reuters

Jami'an tsaron Rundunar juyin-juya-hali ta Iran sun harba makamai masu linzami aƙalla biyu kan jiragen ruwan kasuwanci da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz a ranar Litinin da daddare, a cewar wani rahoto da kafar watsa labarai ta Axios ta rawaito tana mai ambato wasu jami'an Amurka biyu.

An lalata wasu jiragen kasuwanci biyu, sai dai ba a samu asarar rayuka ba, in ji rahoton.

Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci na Jiragen Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta faɗa a safiyar ranar Talata cewa an kai wa tankar wani jirgin ruwa hari a gefen tashar jiragen ruwanta yayin da take tafiya kudu da nisan kilomita 15 daga gabas da yankin Limah na Oman, lamarin da ya haifar da gobara; babu rahoton asarar rai ko wata ɓarna ta muhalli.

Kazalika lamarin ya biyo bayan kawo ƙarshen tattaunawar Amurka da Iran a makon jiya da ba a samu wata ƙwaƙƙwarar matsaya ta ɗorewar zaman lafiya ba, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60 da ake ganin za ta samar da sulhu na diflomasiyya bayan hare-haren Amurka da Isra'ila sun haifar da rikicin.

Masu AlakaTRT Afrika - Miliyoyin mutane sun halarci jana’izar Khamenei a Tehran

A ranar Litinin, Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta cim ma yarjejeniya da Iran ko kuma ta "kammala aikin", yana mai jaddada matsayinsa yayin da Tehran ke nuna rashin amincewa bayan jana'izar tsohon Shugaban Addini na Iran Ali Khamenei.

"Mun shirya harba muku makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa’’ kamar yadda dakarun rundunar juyin-juya-hali na Iran suka yi gargaɗi ta tashar rediyon jiragen ruwa a ƙarshen mako, in ji rahoton Jaridar Wall Street Journals a ranar Litinin.

An zargin ɗaya daga cikin jiragen ruwan da ake kai wa hari na Al Rekayyat ne, wani jirgin ruwan dakon iskar gas mallakin Nakilat, da sashin jigilar kaya na masana'antar LNG ta Qatar ke kula da shi, in ji rahoton jaridar, tana mai ƙari da cewa an kai wa bangaren injin din jirgin hari ne a gefen tashar jiragen ruwa.

"Bangaren injin din jirgin ya kama da wuta kuma ya tirnike da hayaki, yanayin da ya sa ba a iya tantance yawan barnar da aka yi ba. Duk ma'aikatan jirgin suna cikin aminci kuma an tara su a wani gefen jirgin," a cewar WSJ

Jirgin ruwan yana daf da mashigar ruwa, a Tekun Oman, lokacin da aka kai masa hari, in ji WSJ.

Masu zuba jari suna ci gaba da sa ido kan tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan makomar jigilar kayayyaki ta mashigar Hormuz yayin da suke bin diddigin farfadowar fitar da mai daga yankin Gulf.