Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zama a Abuja babban birnin Nijeriya ta dakatar da aiwatar da hukuncin maishari’a Peter Lifu da ya bai wa INEC umarni ta soke rijistar jam’iyyun ADC da APP da AA da AP da kuma ZLP.
Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta Nijeriya ta bayyana hukuncin Babbar Kotun a matsayin tsabar rashin mutunci a harkar shari'a, tana mai cewa alƙalin ya yi biris da umarnin da kotun ta sama ta bayar tun da farko.
Alƙalan kotun sun ce alƙali Lifu ya nuna rashin kunya ta hanyar ci gaba da sauraron ƙara da kuma ba da umarnin duk da umarnin da kotun ɗaukaka ƙarar ta bayar da kuma kasancewar batun a gaban kotun ɗaukaka ƙarar.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce matakin alƙali Lifu ya kasance rashin ɗa’a ga tsarin girmamawa na kotuna.
Ta ce matakin kotun ta ƙasa wata “mafi ƙololuwar rashin ɗa’a ce a harkar shari’a”, tana mai cewa kotun ƙoli ta taɓa yanke hukuncin cewa duk wani alƙalin da ya yi haka “bai dace da alƙalanci ba domin matakinsa ɗaya ne da rashin kunya na shari’a”.
Hukumar Zaɓen Ƙasar INEC ce ta shigar da ƙarar a gaban kotun ɗaukaka ƙara a ranar Talata tana ƙalubalantar hukuncin da babbar kotun ta yanke ranar Litinin na a soke rijistar jam’iyyun.
Jam’iyyar ADC a ta bakin wani mai magana da yawunta ta ce INEC ta sanar da ita matakin na ɗaukaka ƙara.
“Wannan kotun tana da hakki na amfani da ikonta wajen ganin cewa an bi umarninta,” a cewarta.
“A halin yanzu an amince da buƙatar da aka shigar ta dakatar da aiwatar da hukuncin. An dakatar da ɗabbaka hukuncin,” kamar yadda kotun ɗaukaka ƙarar ta ce.
A ranar Litinin ne wata babbar kotu a Abuja ta umarci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta soke rijistar jam’iyar ADC, da APP da AA da AP da ZLP.
Kotun ta ce, jam’iyyun biyar sun gaza cika sharaɗin tsarin mulki da na ci-gaba da kasancewarsu jam’iyyu da kuma shigarsu zaɓuka.
Kotun ta Ɗaukaka Ƙara ta sanya ranar 25 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar.








.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)

