| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Zaftarewar ƙasa ta kashe fiye da mutum 200 a mahaƙar ma'adinai ta Rubaya a Kongo DRC
Ma'aikatar ma'adinai ta tabbatar da cewa kimanin yara 70 na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, inda aka kuɓutar da mutane da yawa da suka jikkata aka kai su wuraren jinya a birnin Goma.
Zaftarewar ƙasa ta kashe fiye da mutum 200 a mahaƙar ma'adinai ta Rubaya a Kongo DRC
Ruwan saman kaman da bakin ƙwarya ya janyo zarftarewar ƙasa a wata mahaƙr ma'adinai a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo / Reuters
5 Maris 2026

Mutum fiye da 200 ne suka mutu bayan wata zaftarewar ƙasa a mahaƙar ma’adinai ta “kwalta” da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya janyo a yankin Rubaya na gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (DRC), kamar yadda ma’aikatar ma’adinan ƙasar ta bayyana.

Ma’aikatar ta ce ruftawar ta faru ne a ranar Talata kuma kimanin yara 70 na cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

An garzaya da yawa daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa wuraren jinya a birnin Goma.

Wani babban jami’i daga ƙungiyar ‘yantawaye ta AFC/M23, wadda ke iko da mahaƙar ma’adinan, ya ba da adadin da bai kai haka ba, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa mutum biyar ko shida ne kawai suka mutu a lamarin.

Rubaya na samar da kashi 15 cikin 100 na ma'adinin kwalta da ake samarwa a duniya, wanda ake sarrafawa zuwa tantalum, wani ƙarfe da ke jure zafi da ake yawan amfani da shi wajen haɗa wayar salula da komfutoci da kuma farfelar samar da lantarki ta iskar gas.

Wurin ya kasance a ƙarƙashin ikon ƙungiyar ‘yantawayen AFC/M23 tun shekarar 2024.

Kwanan baya aka saka shi cikin jerin kadarorin haƙar ma’adinai da gwamnatin Kongo take yi wa Amurka tayi a ƙarƙashin shirin haɗin kai na ma’adinai.

Bala’in na zuwa ne kimanin wata ɗaya bayan irin wannan iftila’in da ya faru a wurin haƙar ma’adinan ya kashe fiye da mutum 200 a ƙarshen watan Janairu.

Ruwan sama mai ƙarfi a Kongo ya haddasa zarftarewar ƙasa da hatsarin haƙar ma’adinai a wurare da ƙananan masu haƙar ma’adinai ke aiki a yanayi mai wuya da hatsari.

Rumbun Labarai
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Shugaban riƙon jihar Kudu maso yammacin Somaliya zai hau kan mulki bayan ajiye aikin shugaba
Sudan ta nemi 'yan ƙasar da suka yi ƙaura zuwa ƙasashen waje saboda yaƙi su koma gida
Hukumar leƙen asirin Somalia ta kashe masu haɗa bama-baman Al Shabab
Mali ta musanta rahoton sakin ’yanta’adda 200 domin samun man fetur
An kasa cim ma matsaya kan sabbin sauye-sauye a tattaunawar WTO a Kamaru
Darasin da Togo ke koya wa sauran kasashe wajen magance cututtukan da aka yi watsi da su
’Yanbindiga sun kashe fararen-hula 16 kusa da iyakar Nijar da Mali
Nijar ta ƙaddamar da sabon katin ɗan ƙasa na zamani mai tambarin AES
Laifi mafi muni: AU ta nemi MƊD ta ɗauki mataki kan biyan diyyar cinikin bayi bayan MƊD ta tabbatar
Ghana ta sake yin bita kan tsarin yaƙi da ta’addanci sakamakon barazanar masu tsattsauran ra’ayi
Rasha ta yi iƙirarin cewa 'yan kwangilar sojin Faransa na da yawa a Afirka