Zaftarewar ƙasa ta kashe fiye da mutum 200 a mahaƙar ma'adinai ta Rubaya a Kongo DRC
Ma'aikatar ma'adinai ta tabbatar da cewa kimanin yara 70 na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, inda aka kuɓutar da mutane da yawa da suka jikkata aka kai su wuraren jinya a birnin Goma.
Mutum fiye da 200 ne suka mutu bayan wata zaftarewar ƙasa a mahaƙar ma’adinai ta “kwalta” da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya janyo a yankin Rubaya na gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (DRC), kamar yadda ma’aikatar ma’adinan ƙasar ta bayyana.
Ma’aikatar ta ce ruftawar ta faru ne a ranar Talata kuma kimanin yara 70 na cikin waɗanda suka rasa rayukansu.
An garzaya da yawa daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa wuraren jinya a birnin Goma.
Wani babban jami’i daga ƙungiyar ‘yantawaye ta AFC/M23, wadda ke iko da mahaƙar ma’adinan, ya ba da adadin da bai kai haka ba, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa mutum biyar ko shida ne kawai suka mutu a lamarin.
Rubaya na samar da kashi 15 cikin 100 na ma'adinin kwalta da ake samarwa a duniya, wanda ake sarrafawa zuwa tantalum, wani ƙarfe da ke jure zafi da ake yawan amfani da shi wajen haɗa wayar salula da komfutoci da kuma farfelar samar da lantarki ta iskar gas.
Wurin ya kasance a ƙarƙashin ikon ƙungiyar ‘yantawayen AFC/M23 tun shekarar 2024.
Kwanan baya aka saka shi cikin jerin kadarorin haƙar ma’adinai da gwamnatin Kongo take yi wa Amurka tayi a ƙarƙashin shirin haɗin kai na ma’adinai.
Bala’in na zuwa ne kimanin wata ɗaya bayan irin wannan iftila’in da ya faru a wurin haƙar ma’adinan ya kashe fiye da mutum 200 a ƙarshen watan Janairu.
Ruwan sama mai ƙarfi a Kongo ya haddasa zarftarewar ƙasa da hatsarin haƙar ma’adinai a wurare da ƙananan masu haƙar ma’adinai ke aiki a yanayi mai wuya da hatsari.