| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Carlos Baleba ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar kuma yana da zaɓin tsawaita ta zuwa shekara shida, a cewar Manchester United.
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Manchester United ta tabbatar da sayen Carlos Baleba daga Brighton a kan fan miliyan 70

Manchester United ta tabbatar da cewa Carlos Baleba ya sanya hannu kan kwangilar shekaru biyar tare da zaɓin ƙara shekara ɗaya.

A ranar Talata Manchester United ta tabbatar da sayen ɗanwasan tsakiyar mai shekaru 22 daga Brighton a kan kuɗi fan miliyan 70 ($95 miliyan) kamar yadda aka ruwaito.

United, ƙarƙashin kocinta Michael Carrick, ta sake fasalin ’yanwasan tsakiya a wannan sabuwar kakar bayan tafiyar Casemiro da kuma sakamakon mummunan raunin da Manuel Ugarte ya samu a gwiwa.

A watan jiya, ƙungiyar ta ƙulla yarjejeniya da Youri Tielemans daga Aston Villa da kuma Andrey Santos daga Chelsea.

United ta ce Baleba, wanda ke buga wa tawagar ƙasar Kamaru wasa, ya sanya hannu kan kwangilar shekaru biyar tare da zaɓin ƙara shekara daya.

‘Na ji daɗi na musamman’

“Na ji wani irin daɗi na musamman wanda ba zai misaltu ba bayan da babban buri na ya cika na taka leda a United. Yin wasa a filin Old Trafford abin alfahari ne a ko da yaushe, amma samun damar yin hakan a matsayin ɗanwasan Manchester United zai zama babban abin alfahari,” in ji Baleba a cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar.

Ba a bayyana takamaiman sharuɗɗan kuɗin ba. Sai dai manema labarai na Birtaniya sun ruwaito cewa kuɗinsa ya kai fan miliyan 65 tare da yiwuwar ƙarin fan miliyan 5.

Manchester United ta ce, a wasanni 31 na Premier League da ya buga a kakar da ta gabata, Baleba ya kasance a cikin kashi 8 na ’yanwasan da suka fi kowa ƙwato ƙwallo da katange ƙwallo, sannan yana cikin kashi 1 na ’yanwasan da suka fi kowa ƙwace ƙwallayen da aka rasa a tsakiya.

“Carlos gwanin ɗanwasan tsakiya ne mai basira,” in ji daraktan wasanni na United Jason Wilcox. “Yana da ƙwarewa ta musamman wacce za ta taimaka sosai wajen inganta tawagarmu.”

Ƙungiyar Hull ta girgiza United bayan da ta doke ta da ci 2-0 a ranar Asabar a makon farko na buɗe kakar Premier League.