| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Isra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila tana amfani da batun tsaro a matsayin hujja na neman mallakar “ƙarin wurare.”
Isra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya
Hakan Fidan ya ceIsra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye / AA

Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya bayyana cewa Isra’ila na ci gaba da shirin “faɗaɗa mamaya” daga yankunan Falasɗinu zuwa ƙasashen Lebanon da Siriya.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila tana amfani da batun tsaro a matsayin hujja na neman mallakar “ƙarin wurare.”

“Isra’ila ba tsaron kanta take nema ba. Isra’ila tana neman ƙarin filaye ne. Gwamnatin Netanyahu tana amfani da batun tsaro ne kawai a matsayin hanzari na mamaye ƙarin ƙasa,” in ji Fidan a wajen taron dandalin diflomasiyya na Antalya (Antalya Diplomacy Forum) a ranar Asabar.

Fidan ya ci gaba da cewa, “Isra’ila ta gina wani tunani na daban a idon duniya, tana ikirarin cewa tana goyon bayan tsaron kanta ne, amma abin ya fito fili, musamman a shekarun baya-bayan nan... lamarin ya wuce haka.”

Ya bayyana cewa matakan da Isra’ila ke ɗauka tun daga yankunan Falasɗinu, Gaza, Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, Kudancin Kudus, sannan yanzu ta nufi Lebanon da Siriya, “shiri ne na ci gaba da mamaya da faɗaɗa iko a yankin.”

“Ina jin ya kamata a dakatar da wannan,” in ji Fidan.

“Dole ne Isra’ila ta sani cewa hanya ɗaya tilo da za ta iya zama cikin zaman lafiya a yankin... ita ce ta bar sauran ƙasashe su mori nasu zaman lafiyar, da ’yancin mallakar ƙasarsu, da kuma cin gashin kansu, maimakon yin amfani da ƙarfin soja a kan waɗannan ƙasashe,” in ji shi.

Shugabannin duniya da manyan jami’an gwamnati ne suka taru a Turkiyya tun daga ranar Juma’a har zuwa ranar Lahadi domin taron diflomasiyya na Antalya — wani babban taro na ƙasa da ƙasa a birnin da ke gaɓar tekun Mediterranean, wanda a wannan shekarar ya mayar da hankali kan yadda za a magance rashin tabbas a duniya.

Taron, wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ta karɓi baƙunci, zai tattauna ne a kan taken “Zana Taswirar Gobe, da Shawo Kan Rashin Tabbas.”

Rumbun Labarai
Asibitin Turkiyya ya kafa 'tarihin' zama na farko a duniya da aka yi dashen hanta da ta haɗa mutum 8
Erdogan ya jinjina wa Turkiyya kan komawa Gasar Kofin Duniya bayan shekara 24
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan
Turkiyya da Saudiyya sun sa hannu kan muhimman yarjejeniyoyi a fannin layin dogo da sufuri
Turkiyya da Nijar sun sanya hannu yarjejeniyoyin hadin kai bayan tattaunawar shugabannin kasashen
An fara shirin gasar Cin Kofin Duniya, yayin da ita ma tawagar Turkiyya ta isa Amurka
Erdogan ya yi bikin cika shekaru 573 da ƙwace Istanbul, ya yi jinina ga Mehmed II
Erdogan ya faɗa wa Iran da Pakistan: A shirye Turkiyya take ta tallafa wa zaman lafiya
Turkiyya da wasu ƙasashe 7 sun yi tir da Isra'ila kan cin zarafin mutanen rukunin jiragen Sumud
Jami'an leƙen asirin Turkiyya sun kama mutum 10 da ake zargin 'yanta'addan Daesh ne a Syria
Turkiyya da Nijeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar haƙar ma’adinai
Erdogan na Turkiyya ya jaddada goyon baya ga 'yancin kan Sudan yayin tattaunawa da Firaminista Idris
Erdogan na Turkiyya ya yi Allah-wadai da kakkausar murya da harin Isra’ila kan jiragen Global Sumud
Belgium na kallon muhimman damarmaki’ don zurfafa alaka da Turkiyya
Erdoğan ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga tsaron UAE yayin da ake cigaba da yaƙi a Gabas ta Tsakiya
Kamfanonin Turkiyya sun ƙulla yarjeniyoyi na kusan dala biliyan 8 a baje-kolin SAHA 2026
Turkiyya na neman shiga kasuwar tsaron duniya da manyan na’urorin yaƙin lantarki na zamani
An fara baje-kolin kayan tsaro da sufurin sararin samaniya na SAHA 2026 a Istanbul
Turkiyya ta zargi Isra’ila da yin 'fashi a teku' bayan tare jirgin ruwan agaji na Gaza
Turkiyya ta yi kira ga ƙasashen Musulmai da su haɗa kai wajen ba da labarinsu da kansu