Isra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila tana amfani da batun tsaro a matsayin hujja na neman mallakar “ƙarin wurare.”
Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya bayyana cewa Isra’ila na ci gaba da shirin “faɗaɗa mamaya” daga yankunan Falasɗinu zuwa ƙasashen Lebanon da Siriya.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila tana amfani da batun tsaro a matsayin hujja na neman mallakar “ƙarin wurare.”
“Isra’ila ba tsaron kanta take nema ba. Isra’ila tana neman ƙarin filaye ne. Gwamnatin Netanyahu tana amfani da batun tsaro ne kawai a matsayin hanzari na mamaye ƙarin ƙasa,” in ji Fidan a wajen taron dandalin diflomasiyya na Antalya (Antalya Diplomacy Forum) a ranar Asabar.
Fidan ya ci gaba da cewa, “Isra’ila ta gina wani tunani na daban a idon duniya, tana ikirarin cewa tana goyon bayan tsaron kanta ne, amma abin ya fito fili, musamman a shekarun baya-bayan nan... lamarin ya wuce haka.”
Ya bayyana cewa matakan da Isra’ila ke ɗauka tun daga yankunan Falasɗinu, Gaza, Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, Kudancin Kudus, sannan yanzu ta nufi Lebanon da Siriya, “shiri ne na ci gaba da mamaya da faɗaɗa iko a yankin.”
“Ina jin ya kamata a dakatar da wannan,” in ji Fidan.
“Dole ne Isra’ila ta sani cewa hanya ɗaya tilo da za ta iya zama cikin zaman lafiya a yankin... ita ce ta bar sauran ƙasashe su mori nasu zaman lafiyar, da ’yancin mallakar ƙasarsu, da kuma cin gashin kansu, maimakon yin amfani da ƙarfin soja a kan waɗannan ƙasashe,” in ji shi.
Shugabannin duniya da manyan jami’an gwamnati ne suka taru a Turkiyya tun daga ranar Juma’a har zuwa ranar Lahadi domin taron diflomasiyya na Antalya — wani babban taro na ƙasa da ƙasa a birnin da ke gaɓar tekun Mediterranean, wanda a wannan shekarar ya mayar da hankali kan yadda za a magance rashin tabbas a duniya.
Taron, wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ta karɓi baƙunci, zai tattauna ne a kan taken “Zana Taswirar Gobe, da Shawo Kan Rashin Tabbas.”