Kamfanin mai na Nijeriya NNPC ya zargi matatar mai ta Dangote da neman taƙaita gogayya da kuma jefa kasuwar man fetur ta ƙasar ga ikon mallakar mutum guda ta hanyar ƙalubalantar lasisin shigo da mai da aka ba wa sauran ‘yan kasuwa da ke gogayya da shi, a cewar takardun kotu da Reuters ta gani.
A cikin bayanan kariya da aka gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, NNPC ya ce amincewa da buƙatar Dangote na soke ko taƙaita izinin shigar da mai ƙasar zai jefa babbar mai samar da mai a Afirka cikin matsala, da rashin daidaiton farashi da kuma hatsarin da ke tattare da tsaron makamashin ƙasa.
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta nemi shiga cikin shari'ar, abin da ya faɗaɗa rikicin shari'ar kan manufofin shigo da mai da kuma matsayin kasuwar matatar mai ta Dangote.
Matatar mai ta Dangote, wacce ta fara sarrafa ɗanyen mai a shekarar 2024, ita ce babbar matatar mai a Afirka.
Rikicin kotun ya zo ne watanni kafin shirin Dangote na gudanar da harkokin matatar mai a watan Satumba, wanda ya ƙara rashin tabbas kan ƙa'idojin kasuwa, gasar shigo da mai da kuma hasashen kuɗaɗen shiga da masu zuba jari za su iya bai wa masana'antar man wacce ke iya tace ganga 650,000 a kowace rana.
Lasisan shigo da mai
Matatar mai ta Dangote ta shigar da ƙara a watan Afrilu tana ƙalubalantar babban lauyan Najeriya, kan lasisin shigo da mai da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta bayar ko ta sabunta ga masu kasuwancin man da kuma NNPC.
Dangote ya bayyana cewa lasisin yana daƙile tace mai a cikin gida kuma ya saɓa da tanade-tanaden Dokar Masana'antar Man Fetur ta Najeriya.
NNPC ya yi watsi da wannan hujja, yana mai cewa dokar ta ba da izinin bayar da lasisin shigo da mai ga kamfanoni masu lasisin tace mai na gida ko kuma masu ingantattun bayanan da aka tabbatar a harkar cinikin ɗanyen mai da tatattacen man fetur a duniya.
Ta ce masu kula da harkokin suna da ikon bayar da izini kan shigo da mai a ƙarƙashin manufar haɗin gwiwa da Nijeriya, kuma babu wani haramcin da aka sanya wa shigo da mai sai dai idan akwai ƙarancin man fetur a cikin gida.
Bukatar man fetur a Nijeriya
Kamfanin NNPC ya kuma ce Dangote bai bayar da "shaida mai inganci, mai zaman kanta ko kuma wanda za a iya tabbatarwa" ba cewa matatar man za ta iya biyan buƙatar man fetur ta Najeriya gaba ɗaya, ko kuma ta tabbatar da wadatar da ake samu a duk faɗin ƙasar ba tare da katsewa ba, kamar yadda takardun kotu suka nuna.
Dangote ya ƙi yin tsokaci yayin da ake ci gaba da shari'ar.
NNPC ya musanta zargin cewa ya yi wa matatar man fetur ta Dangote zagon ƙasa ko kuma ya hana ta ɗanyen mai da gangan, yana mai cewa rabon ɗanyen mai ya dogara ne kan batutuwan da suka hafi yanayin aiki, da kasuwanci, da tsaro da kuma abubuwan da suka shafi sufuri.
Kotun ta shirya sake zaman sauraren ƙarar a makonni masu zuwa.
Masu sayar da mai su ma sun yi adawa da ƙarar ta Dangote, suna gargadin cewa hakan na iya lalata gogayya da samun mai a cikin Nijeriya.














