| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Kenya na binciken abin da ake tunanin guba ce wadda ta kashe giwaye 16
Hukumar ta ce nazari na ɗakin gwaje-gwaje na farko da Jami'ar Nairobi ta yi ya nuna yiwuwar cewa gubar 'cyanide' ce ta haddasa mace-macen.
Kenya na binciken abin da ake tunanin guba ce wadda ta kashe giwaye 16
Maus bincike na kuma duba ko gurɓataccan ruwa ko kuma ciyawa mai guba, sun tak arawa wajen abin da ake tunanin ciyar da guba ne. / AP

Hukumomin da ke kula da dabbobin daji a Kenya suna bincika abin da ake tunanin ciyar da dabbobi guba aka yi bayan mutuwar giwaye 16 a dajin Amboseli-Kimana cikin makonni shida da suka gabata, inda jami’ai suke ƙoƙarin tabbatar wa mutane ranar Juma’a cewa gandun dajin na Amboseli National Park yana cikin amincin da masu ziyara za su iya zuwa.

Hukumar da ke kula da dabbobin dajin Kenya (KWS) ta ce an samu mutuwar giwayen ne tsakanin ranar 24 ga watan Yuni da 31 ga watan Yuli, inda da yawa daga cikin dabbobin suka kasance manya mata da kuma ƙanana da suka nuna alamu na rauni da kuma shanyewar ɓangaren jiki daga ƙafafuwansu na baya kafin su mutu.

"Hukumar da ke Kula da Dabbobin daji ta Kenya ta jajirce wajen tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru da kuma sanar da jama’a abin ta gano a ko wane mataki," in ji Babban Daraktan Hukumar KWS Erustus Kanga a wata sanarwa ranar Jumma’a.

Kwantar da hankula game da damuwa

KWS ta kuma yi yunƙuirn kwantar da hankulan jama’a game da tasirin lamarin ga masu yawon buɗe ido, tana mai cewa: "KWS tana tabbatar wa jama’a da kuma masu ruwa da tsaki a fannin yawon buɗe ido cewa dajin na yawon buɗe ido na Amboseli National Park yana nan a buɗe kuma yana aiki yadda aka saba."

Hukumar ta ce, gwaje-gwaje na farko na ɗakin gwaje-gwaje da aka yi a Jami’ar Nairobi sun nuna cewa guba nau’in ‘cyanide’ ce ta haddasa mace-macen da aka yi nazari a kansu.

Ta ce ana ci gaba da gwajin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ko wanne da kuma nazari kan yadda giwayen suka kai ga gubar.

KWS ta ce an tura tawagogi na lafiyar dabbobi da na kimiyya daga Nairobi da Tsavo da Amboseli bayan an sami mutuwa ta farko ranar 24 ga watan Yuni domin duba dabbobin da lamarin ya shafa, da yin binciken bayan mutuwa da kuma ɗibar wasu ɓangarori na jikinsu da kuma sa ido kan cuta.

Kawo yanzu ana kan bincike kan guba da ƙwayoyin halittu da ma muhalli da suka shafi lamarin.

An ƙaddamar da bincike

Hukumar ta ce wata tawagar ƙwararru ta haɗin gwiwa tsakanin hukumomi tana bincike kan ko magungunan kwaro da ma sauran sinadirai na kare amfanin gona da aka yi amfani da su ba bisa ƙa’ida ba ko kuma aka adana ko aka zubar da su a yankin dajin Kimana da Kuku da Kitenden da ma faɗin dajin Amboseli.

Masu bincike suna kuma dubawa ko gurɓataccan ruwa ko kuma wani nau’i na ciyawa mai guba ne suka zame wa dabbobin guba.

KWS ta ce ababen da aka gano kawo yanzu ba su nuna wata cuta mai yaɗuwa ba, tana mai kawar da damuwar da ake yi cewa mace-macen sun faru ne sakamakon ɓullar annoba mai shafar dabbobin daji.

Muhimmanci na tattalin arziki

Gandun dabbobin dajin ƙasa na Amboseli National Park, wadda ke da nisan kimanin kilomita 240 (mil 149 ) kudu maso gabashin babban birnin Kenya, Nairobi, ɗaya ne daga cikin wuraren kallon namun dajin da suka fi fice, kuma aka fi ziyarta saboda yawan giwayensa, da kuma domin zuwa kallon dutsen Kilimanjaro.

Hukumar ta dabbobin dajin ta ce za ta ci gaba da ba da ƙarin bayanai a duk lokacin da ta samu tabbatattun bayanai kuma ta yi kira ga jama’a masu bayanai masu tushe game da lamarinsu bayar da su ta hanyoyin da ake ba da bayanai a hukumance. 

Rumbun Labarai
Tallafin ƙasashen waje da harin jiragen sama marasa matuƙa sun ƙara tsananta yaƙin Sudan - MDD
Babban hafsan sojin Sudan Burhan na rangaɗi game da shirin yaƙi a fagen yaƙin Blue Nile
Dubban mutane sun yi zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga sojin Nijar bayan dakile yunƙurin tawaye
Hatsarin mota a Masar ya yi ajalin mutum 16 a sanannen yanki mai cike da ‘yan yawon bude ido
Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka ya yi Allah wadai da boren da aka yi a Nijar
An kama ‘yar jarida mai yawan mabiya Denise Dusauchoy ‘yar kasar Kongo a Tanzania
Tebboune ya sake bayyana goyon bayan Aljeriya ga Nijar yayin da ake fuskantar barazanar tsaro
Yadda maganin rana guda zai iya kawo ƙarshen cutar bacci a Afirka
Mayaƙa 200 sun fice daga RSF ta Sudan inda suka sauya sheƙa zuwa rundunar sojin ƙasar
Ghana ta kama mabarata fiye 1,000 a Accra da Kumasi – Hukumar Shige ta Fice ta Ghana
Algeria ta aika jiragen yaƙi huɗu zuwa Jamhuriyar Niger bayan tashin hankali a Niamey
Sojin ruwan Turkiyya da dakarun Somaliya sun ceto jirgin dakon kaya daga 'yanfashin teku
Boren soji a Yamai: AES ta jaddada goyon bayanta ga Nijar, ta yaba wa martanin dakarun tsaro
’Yan a-waren azbinawa sun saki sojojin Mali 60 da suka sace
An ji karar harbe-harben bindiga a kusa da sansanin soji da kuma fadar shugaban kasa a Nijar
Traore ya buƙaci matasan Burkina da su guji bin 'ɓarauniyar hanya' wadda ke kaiwa ga cin amana
Sojojin Sudan sun yi ikirarin harbo wani jirgi maras matuƙi kusa da iyakar Habasha
Gwamnatin Ghana ta yi watsi da gudunmawar cedi miliyan 20 daga kamfanin MTN
Manufar Afirka ta shiga ofis mafi girma a MDD: Ko hakan ba zai iya sake faruwa ba?
Nijar ta cim ma yarjejeniyar gina tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai karfin MW 200