Kasashen Turkiyya da Nijeriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar hakar ma’adinai wacce ake fatan za ta inganta hadaka tsakanin kasashen, wacce kuma za ta amfani kasashen.
Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar da Ministan Bunkasa Albarkatun Kasa na Nijeriya Oladele Henry Alake ne suka sanya hannu a madadin kasashen nasu, yayin da Dele Alake ya kai ziyara Turikiyya don halartar Taron Ma’adinan Kasa na Istanbul Karo na biyu (INRES 2026).
Alparslan Bayraktar ya ce “mun yi imani cewa za mu bunkasa alakarmu da Nijeriya a fannin makamashi da albarkatun kasa, ta hanyar da kasashen biyu za su amfana.”
Me yarjejeniyar ta kunsa?
A wata sanarwa da Mista Bayraktar ya wallafa a shafukna sada zumunta, ya bayyana cewa “ a ganarwarmu da Ministan Ma’adinai na Nijeriya Mr. Oladele Henry Alake da tawagarsa, mun tattauna hanyoyin da za a bi domin samun sakamakon mai alfanu.”
Ya bayyana cewa za a karfafa hadaka tsakanin kasashen, daga hakar ma’adinai zuwa ilimi da musayar fasaha, daga hakar ma’adinai cikin aminci zuwa bunkasa kwarewar ma’aikata da kuma sabon salon zuba jari.
Wata sanarwa da aka fitar ta bayyana cewa, sakamakon wannan yarjejeniya, Turkiyya da Nigeria za su kafa wata hada mai dogon zango a fannin makamashi da hakar ma’adinai ta yadda kasashen biyu za su amfana.
Hadakar za kuma ta kunshi bangarori da suka hada da jan hankali kan zuba jari a bangaren hakar ma’adinai, da fasahar sarrafa ma’adinai, da musayar ilimi da kwararru, da kuma bayar da horo, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma za wanan yarjejeniya za ta yi duba kan yin aiki tare, da bunkasa hanyar hakar ma’adinai cikin aminci da hadaka a fannin kananan ayyukan hakar ma’adinai.















