Nijeriya ta yi gargaɗi kan 'shirin kai harin ta'addanci' kan kayayyakin more rayuwa a Abuja da Neja
Dakarun tsaron Nijeriya suna cikin shirin ko-ta-kwana domin kawar da yiwuwar hari na 'yanta'adda kan kayayyakin more rayuwa a Abuja da jihar Neja, kamar yadda wata sanarwar tsakanin hukumomi da aka rubuta ranar 13 ga watan Afrilu ta bayyana.
Dakarun tsaron Nijeriya suna cikin shirin ko-ta-kwana domin kawar da yiwuwar harin ta’addanci kan kayayyakin more rayuwa Abuja da jihar Neja, kamar yadda wata sanarwar tsakanin hukumomi da aka rubuta ranar 13 ga watan Afrilu ta bayyana kuma kamfanin dillancin labaran AP ya samo daga hukumar hana fasa ƙauri ta kwastom a ranar Laraba.
Wuraren da aka shirya kai hare-haren sun haɗa da filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na birnin tarayya Abuja tare da wani sansanin tsare mutane na soji a jihar Neja mai maƙwabtaka.
“Niyyarsu ita ce su saki ‘yanta’adda da aka tsare da kuma lalata muhimmin kayayyakin more rayuwa na sufurin sama,” in ji sanarwar.
Shirin ya yi kama da irin harin da aka kai Jamhuriyar Nijar a watan Janairu, inda ‘yanta’adda suka kai hari kan wani sansanin sojin sama a Yamai, kamar yadda sanarwar ta bayyana wa jami’an hukumar kwastom.
'Kamanceceniya mai saka damuwa '
“Wani nazari da aka yi kan rahoton ya nuna wani kamanceceniya mai saka damuwa da ke tsakanin yiyuwar kai hari kan filin jiragen sama na Abuja da kuma jerin hare-haren da aka kai kan kayayyakin sufurin jiragen sama a Jamhuriyar Nijar kwannan nan, musamman a Yamai da Tahoua.
Wannan ya nuna yiwuwar niyya ta ‘yanta’adda ta maimaita irin yanayin waɗannan hare-haren a cikin Nijeriya,” in ji sanarwar ta tsakanin hukumomi.
A shekarar 2022, wani hari da aka kai kan gidan yarin da aka ambata ɗin ya hadasa sake fursunoni 879 ciki har da ‘yan wata ƙungiyar ta’addanci 64 , inda ƙungiyar ta’addancin ta ɗauki alhakin kai harin.
“Dakarun soji da ma sauran dakarun tsaro suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma a shirye suke su hana yiwuwar harin,” kamar yadda wani babban jami’in hukumar kwastam wanda ba shi da hurumin magana da ‘yan jarida ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AP.
Ƙungiyar ta’addancin Boko Haram tare da masu alaƙa da ita ce ke son kai hare-hare, in ji sanarwar.
Nijeriya, wacce ita ce ƙasar da ta fi yawan mutane a Afirka, tana fama da matsalar tsaro mai sarƙaƙiya, musamman a arewacin ƙasar, inda barazanar ta’addanci da kuma barazanar wasu ƙungiyoyin ‘yanbindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.