| hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta koma haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.8 a kowace rana kafin Disamba — Shugaban NNPCL
Shugaban kamfanin NNPCL Bayo Ojulari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi bayan ya kai ziyara ga Shugaba Bola Tinubu a Legas. Ya ce ya ziyarci Shugaban ƙasa ne don ya ba shi rahoto kan ayyukan kamfanin NNPCL tun bayan nadinsa a ranar 2 ga Afrilu.
Nijeriya za ta koma haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.8 a kowace rana kafin Disamba — Shugaban NNPCL
Bayo Ojulari ya bayar da tabbacin cewa zuwa ƙarshen shekara za a cim ma wannan buri
6 Oktoba 2025

Babban Daraktan Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Bayo Ojulari, ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa zuwa ƙarshen shekara, ɗanyen man fetur ɗin da Nijeriya ke haƙowa a duk rana zai kai ganga miliyan 1.8.

Ojulari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi bayan ya kai ziyara ga Shugaba Bola Tinubu a Legas.

Ya ce ya ziyarci Shugaban ƙasa ne don ya ba shi rahoto kan ayyukan kamfanin NNPCL tun bayan nadinsa a ranar 2 ga Afrilu.

 “Tare da wasu gyare-gyaren da muka yi a watan Agusta da Satumba, dukkan su ana sa ran su dawo aiki a wannan watan.
“Muna sa ran kafin ƙarshen shekara za mu kai akalla ganga miliyan 1.8 a rana,” in ji Ojulari.

Rikicin matatar Dangote da PENGASSAN

Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (PENGASSAN) da Kamfanin Man Dangote sun samu saɓani kan zargin korar ma’aikatan matatar ‘yan Nijeriya fiye da 800 tare da maye gurbinsu da ƙwararru na ƙasashen waje.

A ranar 26 ga Satumba, ƙungiyar ta ba da umarni ga membobinta su fara yajin aiki na ƙasa baki ɗaya sakamakon matakin na Dangote.

Bayan kwana biyar, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan Rukunin Kamfanonin Dangote ya amince ya mayar da ma’aikatan da aka kora, bisa shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi.

Ojulari ya nuna ta’aziyya kan asarar da aka yi a cikin ɗan gajeren lokacin da yajin aikin ya ɗauka.

Sakamakon faruwar wannan lamarin, Ojulari ya jajanta game da irin asarar da aka tafka ta ɗan ƙaramin lokaci sakamakon wannan yajin aikin.

“Abin takaici ne yadda rikicin Dangote da PENGASSAN ya jawo yajin aiki. Kamar yadda kuka sani, idan aka yi yajin aiki kuma ma’aikata masu kula da muhimman wurare ba su nan, ba zai yiwu a ci gaba da aiki yadda ya kamata ba.

“A wannan yanayi, mun rasa fiye da ganguna 200,000 a kowace rana da aka jinkirta.

“Haka kuma an rage fitar da iskar gas, kuma yajin aikin ya shafi wutar lantarki ta kusan megawatt 1.2,” in ji shi.

Gwamnatin Tarayya ta sa baki

A ranar 30 ga Satumba, Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Ƙasa, Nuhu Ribadu, ta shiga tsakani domin sasanta rikicin.

An ce taron ya kasance mai albarka, inda ƙungiyar ta yarda da janye yajin aikin, yayin da ma’aikatan da aka kora aka mayar da su.

Rumbun Labarai
Nijeriya ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 15% kan shigar da fetur da dizal cikin ƙasar
'Musulmai ne Boko Haram ta fara yi wa ɓarna': AU ta yi watsi da Trump kan kisan kiyashi a Nijeriya
Za mu bai wa kowane jami'in soja da ke bakin aikinsa kariya  - Ministan Tsaron Nijeriya
An kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1,000 a Nijeriya
‘Yan wasan Super Eagles sun ƙaurace wa atisaye kan rashin biyansu alawus
Jiragen yaƙin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da ɓarayin daji a Borno da wasu jihohin Arewa
Babu abin da za mu rasa idan Nijeriya ta daina hulɗa da Amurka – Sheikh Gumi
Damuwa kan kutsawar 'yan bindiga Jihar Kano
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da Boko Haram ta yi garkuwa da su
INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra
Gwamnatin Nijeriya ta amince a ci bashin dala 396 domin inganta kiwon lafiya da ayyukan jinƙai
An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar