Yadda Biteye na Senegal ke amfani da ƙwallon ƙafa don samun waraka ga ƙwaƙwalwa

Suna kiran sa da malam mahaukaci da ke horar da ‘yan kwallo. A mafi yawan lokuta - ko'ina da gaske - wataƙila za a yi la'akari da hakan a matsayin maras dacewa.

By
Ya samar da ƙungiya mai kyau tsawon shekaru, yana zaɓar ‘yan wasansa daga asibitocin kula da masu tabin hankali da ke babban birnin Senegal. / TRT Afrika

Wani matashi mai manufar hidimtawa al’umma da tausaya wa masu fama da ciwon kwakwalwa ya taimaka wajen mayar da masu cutar da ake kyamata zuwa ‘yan kwallon kafa masu kyau da suke samun horo, suke tafiya da a yanzu ke wakiltar Senegal a gasar duniya.

Suna kiran sa da malam mahaukaci da ke horar da ‘yan kwallo. A mafi yawan lokuta - ko'ina da gaske - wataƙila za a yi la'akari da hakan a matsayin maras dacewa.

Amma Malick Biteye ya mayar da abin da zai iya zama izgili zuwa wani abu mafi kusa da matsayin girmamawa. malam mai horarwa mahaukaci yabo ne ga aikin da ya yi a filayen ƙwallon ƙafa a faɗin Dakar tsawon kusan shekaru goma.

Biteye, ma'aikacin zamantakewa, yana horar da mutanen da ke fama da rashin lafiyar kwakwalwa. A wajen sa, ƙwallon ƙafa ba wai kawai magani ba ce a filin kwallo. Ya samar da ƙungiya mai kyau tsawon shekaru, yana zaɓar ‘yan wasansa daga asibitocin kula da masu tabin hankali da gidaje a kusa da babban birnin Senegal, yana amfani da ka'idoji da aka aro daga kwamitocin ƙwallon ƙafa na duniya na lafiyar kwakwalwa.

'Yan wasansa suna yin atisaye akai-akai, suna fafatawa a ƙasashen waje, kuma sun ƙulla alaƙa mai ƙarfi har wasu waɗanda ke ɓacewa daga gidajensu na tsawon kwanaki har yanzu suna zuwa don yin atisaye.

Abin da ya fara da yakinin wani mutum - cewa wasanni na iya bayar da wani abu da magani kaɗai ba zai iya ba - ya zama ƙungiyar da ke wakiltar Senegal a hukumance a wasanni da gasar ƙasa da ƙasa.

Abin da ya ƙara burge ni shi ne cewa yana aiki ba tare da wani tallafi daga gwamnati ba, kodayake yana damuwa game da tsawon lokacin da zai iya ɗauka yana aikin.

"Da yake ina da yara uku da yake tarbiyyar su, zai yi matuƙar wahala na ci gaba da aikin ba tare da aiki ko abokin tarayya da zai tallafa mana ba," ya fada wa TRT Afrika.

Neman manufa

Rayuwar Biteye har zuwa inda yake yanzu ba a shirya ta ba. Bayan kammala makarantar sakandire, ya tafi Italiya ya samu horo a matsayin mataimakin kiwon lafiya, inda ya sami sabbin ra'ayoyi da suka tsara yadda yake kallon duniya.

"Na kasance mai abokantaka da yara da maƙwabtana," in ji shi. "Ina koma wa Senegal, sai na ji ina son shiga cikin ayyukan al'umma."

Sabon ra'ayinsa na haɓaka ƙungiyar ƙwallon ƙafa wadda ta ƙunshi mutanen da ke fama da cututtukan tabin hankali, duk da haka, ya ɗauki shekaru kafin ya cika burinsa.

"Tabbatar da lafiya da amincewar iyali na da muhimmanci ga tsarin ɗaukar ma'aikata," in ji Biteye.

Gina tsari mai kyau

Dabi’ar Biteye ta ƙaunar yin hidima ga jama’a, kungiyar Thérapie Foot, ta girma tsawon shekaru inda ta zama ƙungiya mai kyakkyawan shugabanci.

Wasu masu horarwa biyu suna aiki tare da matashin wanda ya kafa ƙungiyar, suna bin ƙa'idoji daga Kwamitin Kwallon Kafa na Duniya kan Lafiyar Hankali waɗanda aka tsara don ƙara tasirin magani na wasanni ga waɗanda ke fama da cututtukan tabin hankali.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta lura cewa motsa jiki "yana rage hatsarin cututtukan kwakwalwa" kuma "yana taimakawa wajen katse tunani marar kyau da ke da alaƙa da gajiyawar ruhi, baƙin ciki, da damuwa".

A filin wasa, hanyar Biteye ba ta bambanta da abin da masu horarwa a mataki mafi girma na wasanni ke bi ba.

Horon da ake bayarwa ya dogara ne akan ƙa'idoji da aka kafa. Wasannin suna cikin tsari. Yanayi yana ci gaba da kasancewa mai kayatarwa, amma ladabtarwa na da muhimmanci, kuma masu horarwa suna kasancewa masu lura da buƙatun kowane ɗan wasa. Biteye ya gamsu cewa daidaita tsakanin tsari da tausayi yana sanya tsarinsa ya yi kyau.

"Wani lokaci, yaran suna guduwa daga gida suna yawo a kan tituna. Suna iya zama a waje na tsawon kwanaki ba tare da dawowa gida ba, amma ba sa rasa samun horo," ya shaida wa TRT Afrika, muryarsa ta yi kama da wanda ke cikin alfahari. "Bugu da ƙari, suna ƙirƙirar ƙungiyar abokai masu ƙwazo waɗanda ke ƙaunar ƙwallon ƙafa."

Kalubalen kudade

Tawagar Thérapie Foot ta saba wakiltar Senegal a gasannin kasa da kasa na marasa lafiya masu tabin hankali. Duk da haka, babu goyon bayan gwamnati a hukumance. A wajen Biteye, wanda ya dauki nauyin yawancin aikin da kansa tare da taimakon wasu abokan hulda, lamarin ya zama wanda zai dore ba.

"Lokacin da ka yi sadaukarwa kuma ka san cewa za ta iya amfanar da dukkan al'umma da kuma canza rayuwar mutane, ba za ka iya ja da baya ba," in ji shi. "Amma idan aka ci gaba ba tare da goyon baya mai dore wa ba, a gaskiya, yana da matukar wahala."

Ya tsaya cak, ya yi dogon nishi, sannan ya girgiza kansa lokacin da aka tambaye shi ko yana da shirin shawo kan matsalar.

Akwai abin da ya faru da ya sanya shi a damuwa. A shekarar 2018, an yi shirin kungiyar za ta ta tafi zuwa Italiya don halartar gasar kasa da kasa. Rashin kudi ya hana tafiyar. Wasu iyaye, cikin takaici da fushi, sun janye 'yan uwansu daga shirin.

A watan Nuwamba na wannan shekarar, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da Kwamitin Kwallon Kafa na Duniya kan Lafiyar Hankali za su shirya gasar cin kofin duniya ga marasa lafiya da ke da tabin hankali a Maroko. Biteye yana mafarkin kai 'yan wasansa don halartar gasar.

Mafarki ma yana buƙatar kuɗi, kuma a yanzu, wannan shi ne ginshiƙin da Biteye ba zai iya cim ma wa ba.