Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata

Aƙalla mutum 1,075 suka rasu a Nijar sannan 4,393 suka ji munanan raunuka, 8,163 suka ji raunuka masu sauƙi a shekarar 2023, sakamakon jerin hatsarin ababen hawa 7,671 da suka faru a faɗin ƙasar, bisa ga bayanan da hukumar kiyaye haɗura ta Nijar.

By
Haka kuma rahoton ya nuna cewa matsakaicin adadin mutuwar da ke faruwa sakamakon haɗarin mota a duniya shi ne 18.2 cikin 100,000 na jama’a

Aƙalla mutum 1,075 suka rasu a Nijar sannan 4,393 suka ji munanan raunuka, 8,163 suka ji raunuka masu sauƙi a shekarar 2023, sakamakon jerin hatsari na ababen hawa 7,671 da suka faru a faɗin ƙasar, bisa ga bayanan da hukumar kiyaye haɗura ta Nijar (ANISER) ta fitar.

Jaridar Sahel ta Nijar a ranar Talata ta ruwaito ƙididdigar ANISER inda ta ce “A shekarar 2023, Nijar ta yi rijistar hatsarori 7,671 da suka janyo mutuwar mutane 1,075, raunukan da suka tsananta ga mutane 4,393 da kuma raunuka masu sauƙi ga mutane 8,163.

Daga cikin dalilan hatsarorin akwai gudu fiye da kima, rashin bin alamomin hanya, shan kayan maye, haɗa mutane da kaya cikin mota ɗaya, da kuma lodi fiye da ƙima.”

Domin magance wannan matsala, hukumomin da ke kula da harkokin sufuri a Nijar sun ɗauki wasu matakai, ciki har da kafa kwamitin fannoni da dama wanda ya ƙunshi jami’an gwamnati domin bincikar dalilan hatsarori da kuma bayar da shawarwari na gajeren lokaci, matsakaici, da dogon lokaci.

Kwamitin kuma yana da alhakin ba da shawarwari kan sabunta motocin da ake amfani da su a ƙasar domin rage yawan haɗuran hanya sosai.

A cewar jaridar gwamnati, “Baya ga waɗannan matakan, akwai wasu shirye-shirye da ake aiwatarwa don magance haɗuran mota, ciki har da Tsarin Kasa na Kiyaye Hanya na 2014–2025, inganta tsarin duba lafiyar motoci, sabunta tsarin horarwa da gwaji ga masu neman lasisin tuƙi, kafa tsarin binciken tsaro kan gine-ginen hanyoyi, tabbatar da bin dokokin tsaro kamar sanya hular kwano da belt ɗin kujera, da kuma ƙarfafa hukunta masu karya dokokin hanya.”

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da aka wallafa a shekarar 2018 ya nuna cewa a duniya baki ɗaya, hatsarorin mota sun janyo mutuwar mutane miliyan 1.35, raunuka miliyan 50, da asarar tattalin arziki da ta kai dala biliyan 518, wanda ya yi daidai da CFA biliyan 291,116.

Haka kuma rahoton ya nuna cewa matsakaicin adadin mutuwar da ke faruwa sakamakon haɗarin mota a duniya shi ne 18.2 cikin 100,000 na jama’a — ma’ana mutum ɗaya yana mutuwa duk bayan dakikoki 24 a hanyoyin duniya.

A cewar dai wannan rahoton, “Afirka ce ke kan gaba a yawan mutuwar da ke da nasaba da haɗuran mota, da mutuwar 26.6 cikin 100,000 na jama’a, yayin da Nijar ke matsayi na 20 a cikin ƙasashe 49 na Afirka da aka yi nazari a kansu, da mutuwar 26.2 cikin 100,000 na jama’a.”