| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Sojojin Yemen sun kaddamar da hare-hare 875 kan Houthi, sun ce sun kashe 130 daga cikin mayakan
Rundunar Sojin Yemen ta ce jiragen yaƙi, jirage marasa matuƙa da manyan bindigogin atilare sun taimaka wajen kai hare-haren ƙasa, inda aka lalata motoci da kayan aikin soji guda 50, ciki har da na'urorin harbo makamai masu linzami.
Sojojin Yemen sun kaddamar da hare-hare 875 kan Houthi, sun ce sun kashe 130 daga cikin mayakan
Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen na ci gaba da gudanar da yaƙi a fagagen daga na kudanci da yammacin ƙasar daban-daban, in ji sojin Yemen

Dakarun gwamnatin Yemen sun kai hare-haren soji guda 875 kan mayakan Houthi cikin 'yan sa'o'in da suka gabata, inda suka yi ikirarin kashe ko raunata mayaƙa 130 na ƙungiyar.

Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar, Majed al-Nazili, ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X cewa hare-haren haɗin gwiwar da aka kai, an kai su ne a sansanonin mayakan Houthi, dakarunsu na ko-ta-kwana da kuma kayan yaƙinsu, a wani ɓangare na farmakin soji mai suna Operation Dawn of Yemen.

Al-Nazili ya ce jiragen yaƙi, jirage marasa matuƙa da manyan bindigogin atilare sun taimaka wajen kai hare-haren ƙasa, inda aka lalata da kayan aikin soji guda 50, ciki har da na'urorin harbo makamai masu linzami.

Rikici ya ƙara tsananta a fagen daga

A lardin Taiz da ke kudu maso yammacin Yemen, dakarun gwamnati tare da mayakan ƙungiyar Popular Resistance sun ci gaba da daƙile hare-haren mayakan Houthi, yayin da suke kai hare-hare kan wuraren da ƙungiyar ke tattara mayaƙanta da kuma hanyoyin jigilar kayayyakinta na yaƙi.

Haka kuma, wasu rundunonin soji sun fafata da ƙarin dakarun Houthi na ko-ta-kwana a lardunan Marib da Al-Jawf.

Rundunar sojin ta kuma tabbatar da cewa dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen na ci gaba da gudanar da yaƙi a fagagen daga na kudanci da yammacin ƙasar daban-daban.

Sojojin sun ce suna ɗaukar matakan kariya na musamman domin kare fararen-hula da muhimman ababen more rayuwa na fararen-hula da ke kusa da wuraren yaƙin.

Yemen na ci gaba da fama da rikici tun shekarar 2014, lokacin da mayakan Houthi suka ƙwace iko da babban birnin ƙasar, Sana'a, da kuma yankuna masu yawa.

A shekarar 2015, ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ta shiga yaƙin domin mara wa gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita baya.

Sabon rikicin soji tsakanin dakarun gwamnati da mayakan Houthi ya ƙara tsananta sosai a watan Yuli, bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka fara aiwatarwa tun shekarar 2022.