Ma'aikata 'yan ci-rani 'yan kasar Bangladesh aƙalla 16 ne suka mutu lokacin da gobara ta tashi a ranar Lahadi a wata masana'antar ƙera kujeru a babban birnin Saudiyya, Riyadh, in ji Ma'aikatar Kula da 'Yan Ci-rani da Aikin yi a Ƙasashen Waje ta Bangladesh, tana rawaito sashen kashe gobara na Saudiyya.
Ministan Kula da 'Yan Ci-rani da Aikin yi a Ƙasashen Waje, Ariful Haque Chowdhury, ya bayyana matuƙar baƙin ciki da ɓacin rai kan mutuwar.
Goma daga cikin waɗanda abin ya shafa sun fito ne daga gundumar Naogaon ta arewacin ƙasar, yayin da sauran suka fito daga gundumomin arewa da yammacin Natore da Rajshahi, a cewar ma'aikatar.
"Irin wannan mutuwar mai ban tausayi da ta samu 'yan ci-rani da ke aiki a Saudiyya don neman abin rufawa kai asiri abin tausayi ce. Gudunmawar da suke bayarwa ga tattalin arzikin ƙasar na da yawa," in ji Chowdhury a cikin sanarwar.
Ya ce Ofishin Jakadancin Bangladesh a Saudiyya na ci gaba da tuntuɓar wurin da hatsarin ya faru da kuma hukumomin yankin.
An umarci jami'an da abin ya shafa da su gaggauta mayar da gawarwakin 'yan ci-ranin da kuma tabbatar da duk wani taimako da gwamnati ke bayarwa da kuma diyya ga iyalansu.
A halin yanzu, Ma'aikatar Harkokin Waje ta Bangladesh ta ce tana sa ido sosai kan lamarin tare da bayar da duk wani taimako da ake buƙata.
Jami'an Ofishin Jakadancin Bangladesh da ke Riyadh sun je wurin da ibtila’in ya faru, kuma suna aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin Saudiyya don gano mamatan da kuma kammala ayyukan da suka wajaba don mayar da gawarwakinsu gida.
Saudiyya ta kasance babbar cibiyar ma'aikatan 'yan ci-rani na Bangladesh, inda kimanin 'yan ƙasar miliyan 3.5 ke zaune tare da yin aiki a Saudiyya.
Ma'aikata 'yan ci-rani na Bangladesh sun aika da fiye da dala biliyan 2.7 zuwa gida a bara, inda yawancinsu ke yin ayyukan da ba sa buƙatar ƙwarewa sosai.




















