| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Tsohon Shugaban Iran Ahmadinejad ya musanta rahotannin cewa Isra'ila ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa aiki
A cikin wata sanarwa, ofishin Ahmadinejad ya zargi jaridar New York Times da wallafa rahotannin da aka ƙiƙira don yaudarar ra'ayin jama'a da ƙara haddasa rarrabuwar kai a cikin gida a Iran.
Tsohon Shugaban Iran Ahmadinejad ya musanta rahotannin cewa Isra'ila ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa aiki
Rahoton ya zargi cewa wannan shirin wani ɓangare ne na babban yunkurin Isra'ila na kawo sauyin gwamnati a Iran

Tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad a ranar Talata ya ƙaryata wani rahoto na The New York Times da ke zargin cewa hukumar leken asiri ta Isra'ila, Mossad, ta nemi ɗaukar shi aiki haka kuma an yi masa ɗaurin-talala, inda ya bayyana ikirarin a matsayin “ƙarya tsagwaronta.”

A cikin wata sanarwa, ofishin Ahmadinejad ya zargi jaridar da wallafa rahotannin da aka ƙiƙira don yaudarar ra'ayin jama'a da ƙara haddasa rarrabuwar kai a cikin gida a Iran.

Ofishin ya kuma ƙaryata cewa Ahmadinejad yana ƙarƙashin ɗaurin-talala, inda ya ce wannan ikirarin an ƙirƙire shi ne domin tallafa wa abin da suka kwatanta a matsayin ikirarin jaridar “marar ma'ana”.

“Muna musanta gaba ɗaya dukkan waɗannan ƙarairayin da The New York Times ta yayata,” in ji sanarwar.

The New York Times ruwaito a ranar Litinin ta ruwaito cewa Mossad ta yi ƙoƙari a shekarun baya don ta rinjayi Ahmadinejad ya haɗa kai da Isra'ila kuma sun ɗauke shi a matsayin mai yiwuwar wanda zai jagoranci Iran.

Rahoton ya zargi cewa wannan shirin wani ɓangare ne na babban yunkurin Isra'ila na kawo sauyin wamnati a Iran bayan hare-haren farko da aka kai kan manyan shugabannin Iran.

“A 'yan shekarun nan, bisa ga jami'an Amurka, Isra'ila ta biya Ahmadinejad a asirce domin gidaje da tafiye-tafiye, kuma ma'aikatan leken asiri na Isra'ila sun haɗu da shi a ƙasashen waje a lokuta da dama, ciki har da ziyarori a Budapest,' in ji rahoton.

Jaridar ta yi ikirarin cewa ƙoƙarin ya kai kololuwa a ƙarshen watan Fabrairu, a ranakun farko na yaki tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran, lokacin da ake zargin jami'an leken asiri na Isra'ila sun ƙoƙarta cire Ahmadinejad daga Tehran a wani shiri na taimakawa juyar da gwamnatin Iran da mayar da shi shugaba.

A cewar rahoton, wani harin jirgin sama na Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu ya faɗa kan gidan Ahmadinejad, sannan ya shafi gidan da dogaransa ke amfani da shi da kuma motarsa mai sulke.

Jami'an Iran guda huɗu masu mukami sun ce wata mota baƙa ƙirar Peugeot ta iso bayan harin, ta ɗauki tsohon shugaban ƙasar kuma ta kai shi zuwa wani wuri ɓoyayye na sirri cikin Iran, in ji rahoton.

Ta ambaci jami'an Amurka da na Iran da suka san yadda aikin ya kasance, jaridar ta zargi motar cewa ma'aikatan Mossad ne suka tuka ta.

A makon da ya gabata, Ahmadinejad, wanda ya rike kujerar shugaban ƙasar Iran daga 2005 zuwa 2013, ya halarci jana'izar marigayi Shugaban Kasa na Iran Ali Khamenei a bayyanar da ya yi a fili na farko tun bayan yakin Amurka da Isra'ila kan Iran.

Rumbun Labarai
Yaƙin Yemen ya raba fiye da mutum 100,000 da muhallansu — Majalisar Ɗinkin Duniya
Iran ta ba da umarni a yi shirin yaƙi da tsagaita wuta da yanayin bayan yaƙi ga dukkan ƙasar
Hukumar sa ido kan Pentagon ta ce yaƙin Iran ya jawo ƙarancin makamai 'masu mahimmanci'
Saudiyya ta ce wasu jirage marasa matuƙa da aka aika daga Iraƙi sun kai hari kan wani bututun mai
Amurka ta yi biris da kiran Saudiyya na kai wa Houthi hari, ta ce za ta ba da taimakon bayanan sirri
Isra’ila ta sake jaddada barazanar kai hari wuraren makamashin Iran
Ƙin amincewar Ingila da mamayar da Isra’ila ke yi ba bisa doka ba ya kawo babban sauyi- Wani Malami
Trump ya ce Amurka tana samun nasara a kan Iran kuma za ta kira Mashigar Hormuz da 'Mashigar Trump'
Iran ta kai hari kan sansanin sojoji da jiragen yaƙin Amurka da ke Jordan
Ministocin Larabawa sun yi watsi da shirin korar Falasdinawa, suna neman a kare Gaza
Iran ta yi gargadin cewa matsin lambar Amurka na iya sakawa a hana jiragen ruwa shiga tekun Gulf
Masu aikin Umrah biyu sun rasu, 25 sun jikkata bayan bas ɗauke da 'yan ƙasar Masar ta yi hatsari
Dalilan da suka sa ya kamata Uganda ta sake tunani kan tura dakaru Gaza
Jaridar Isra'ila ta ba da shawarar yafe wa matasan Amurka bashi don su shiga yaƙin Iran
Ben-Givir na Isra'ila ya gabatar da shirinsa na korar Falasɗinawa 1.8m daga Gaza a shekara bakwai
Trump na duba yiwuwar ayyana kawo ƙarshen yaƙi da Iran
Amurka na yaƙar Iran ne don kare ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya da ƙasashen Yamma - Trump
Iran ta ce harin bam na Amurka a wajen bikin aure a Hormozgan ya kashe fararen hula
Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya buƙaci ’yan kasa su rage amfani da fetur
Iran ta ce ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke UAE, ta harbo jiragen leken asiri na ƙasar