Nijeriya ta bukaci a saki ’yan ƙasarta 42 da aka kama a Mozambique
Rahotanni sun nuna cewa an kama ’yan Nijeriyar ne yayin wani samame da aka kai a wata kasuwar kayan ababen hawa (Spare parts), inda aka kama su yayin da aka ƙyale ’yan kasuwar sauran ƙasashe da ke wurin.
Gwamnatin Nijeriya ta yi kira da a gaggauta sakin wasu ’yan ƙasarta 42 da aka bayar da rahoton kama su a ƙasar Mozambique ba tare da wani takamaiman laifi ba, abin da ya tayar da hankulan hukumomin ƙasar, inda suka bayyana hakan da ƙin jinin baƙi.
Shugabar Hukumar ’Yan Nijeriya mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ce ta yi wannan kiran, kuma ta yi Allah wadai da kamun.
Ta buƙaci mahukuntan Mozambique su saki mutanen ko kuma su gurfanar da su a gaban kotu idan har akwai laifin da suka aikata.
A wata sanarwa da aka fitar a birnin Abuja ranar Lahadi, wadda kakakin hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya sanya wa hannu, Dabiri-Erewa ta ce tsare ’yan Nijeriyar ba tare da bayyana laifinsu ba, abin damuwa ne.
“Abin takaici ne a ji cewa ’yan Nijeriya kaɗai aka je aka kama,” in ji ta. “Idan har sun karya doka, ya kamata mahukunta su gurfanar da su a gaban kotu.”
A cewar hukumar, rahotanni sun nuna cewa an kama ’yan Nijeriyar ne yayin wani samame da aka kai a wata kasuwar kayan ababen hawa (Spare parts), inda aka kama su yayin da aka ƙyale ’yan kasuwar sauran ƙasashe da ke wurin.
“Kamen ’yan Nijeriya kaɗai da aka yi farat ɗaya yana nuni da cewa an yi kamen ne saboda nuna ƙyama ko wariya ga ’yan ƙasar Nijeriya,” in ji Dabiri-Erewa. Ta yi kira ga mahukuntan Mozambique da su “gaggauta sakin ’yan Nijeriyar da aka kama ko kuma su bar doka ta yi aikinta.”
Hukumar NiDCOM ta ce an tabbatar da cewa waɗanda aka kama suna zaune ne a ƙasar bisa ƙa’ida, sannan kuma Antoni Janar na Nijeriya ba shi da labarin wata tuhuma da aka shigar kansu ba.
Kazalika hukumar ta ambato rahotannin da ke cewa an doki waɗanda aka tsaren lokacin da ake ƙoƙarin kama su, kuma an kwashe musu kayayyakinsu, sannan wasu da dama sun kamu da rashin lafiya a gidan yari kuma suna buƙatar kulawar likitoci.
Dabiri-Erewa ta buƙaci mahukuntan Mozambique da su tabbatar da tsaro da lafiyar waɗanda aka tsare yayin da ake ƙoƙarin warware wannan matsalar.