Libya, ƙasa mai arzikin makamashi a Arewacin Afirka wadda take da mafi girman arzikin mai a Afirka, ta faɗa cikin mummunan yaƙin basasa a shekarar 2014 tsakanin ƙungiyoyin yammaci da gabashin ƙasar masu adawa, shekaru uku bayan juyin mulki da kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar Muammar Gaddafi.
Duk da faɗan da ake yi a tsakanin dakarun da ke adawa da gwamnati, gwamnatin da aka amince da ita a duniya a Tarabulus ta ci gaba da riƙe halascinta, inda ta sanya hannu kan yarjejeniyoyi masu muhimmanci da ƙasashe kamar Turkiyya.
Duk da haka, a cikin 'yan shekarun nan, tattaunawar siyasa tsakanin gwamnatocin da ke adawa da gwamnati ta sami karɓuwa, inda Turkiyya ke tallata manufarta ta "Libiya ɗaya" da kuma tallafawa kusanci tsakanin ɓangarorin biyu don haɗa ƙasar da ta wargaje a ƙarƙashin gwamnatin tsakiya ɗaya.
A watan Afrilu, bangarorin da ke hamayya da juna na gabas da yamma sun cim ma yarjejeniya kan kasafin kudin kasa ɗaya domin raba kudaden shiga masu yawa da ake samu daga man fetur, matakin da ke nuna ci gaba a hanyar sake hadewar kasar.
A watan Agusta, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya kai ziyara mai muhimmanci a Libya, inda ya gudanar da tattaunawa ba kawai a Tarabulus — hedikwatar gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita a yammacin kasar—ba, har ma a Benghazi, wato sansanin gwamnatin gabas karkashin jagorancin Khalifa Haftar, Janar din da ke jagorantar Rundunar Sojin Kasar Libya (Libyan National Army).
"Yana da matukar muhimmanci 'yan uwanmu na Libya su gina makomarsu cikin 'yanci, tsaro, da wadata. Bisa tsarin da Shugabanmu Recep Tayyip Erdogan ya shimfida, za mu ci gaba da tallafawa tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin yankunan yammaci da gabashin Libya, tare da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaban kasar," in ji shi bayan kammala tattaunawarsa a Libya.
Manufar samun ‘Libya Guda Daya’
Makonni biyu bayan tarukan da Fidan ya gudanar a Libya, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da wani tsari mai dauke da jadawalin shekaru biyu na gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, da hadewar hukumomi, da kuma sake fasalin hukumar zabe; matakin da ke nuna cigaba wajen sake hadewar kasar.
"Yadda a yanzu kasar Turkiyya ke samun damar tattaunawa da bangarorin biyu da suka raba kan Libya, abu ne mai matukar amfani," in ji Salah Bakkoush, wani mai sharhi kan harkokin siyasar Libya, yayin da yake zantawa da kafar TRT World.
"Tasirin Turkiyya zai fi bayyana sosai idan har tattaunawar da take yi da bangarorin biyu ta haifar da hadewar hukumomi, maimakon amincewa da ci gaba da kasancewar hukumomi masu cin gashin kansu da ke aiki a layi daya amma daban-daban," in ji Bakkoush, wanda kuma tsohon mai ba da shawara ne ga Babban Majalisar kasar Libya.
Bakkoush ya lura da yadda bangarorin siyasa masu adawa da juna a Libya ke kara nuna sha'awar cim ma matsaya ta sulhu.
Sai dai, ya yi gargadin cewa hada cibiyoyin iko masu hamayya a karkashin ikon gwamnati daya zai kasance da wahala, saboda har yanzu ba a warware batun "ikon hukumomi" tsakanin bangarorin biyu ba.
Bayan ziyarar Fidan, an samu karuwar hulda ta diflomasiyya tsakanin Libya da Turkiyya. Shugaban hukumar leken asirin Turkiyya, Ibrahim Kalin, ya gana da mukaddashin ministan tsaron Libya, Abdussalam Zubi, a birnin Istanbul ranar Asabar domin tattauna kokarin da ake yi na hada hukumomin kasar wuri guda.
A ranar Talata, Shugaba Recep Tayyip Erdogan shi ma ya gana da Mohamed Menfi, shugaban Majalisar Shugabancin Libya, a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 a birnin New York, inda ya jaddada muhimmancin tattaunawa ta kasa da kuma sulhu.
"Libya da ta rabu gida-gida tana haifar da rashin tsaro; amma Libya mai cikakken ikon kanta za ta iya shawo kan hakan," in ji Bakkoush. "Yayin da Libya ke kara samun nasarar dawo da iko daya kan hukumominta, iyakokinta da kuma jami'an tsaronta," hakan zai kara bai wa kasar damar dakile hanyoyin safara ba bisa ka'ida ba tare da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, in ji mai sharhin na Libya.
Alakar Ankara-Benghazi
Kokarin da Turkiyya ke yi na haɗa kan Libya ya fara aiki musamman tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Oktoban 2020 tsakanin Gwamnatin Yarjejeniyar Ƙasa (GNA) da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ita da ke Tarabulus da Rundunar Sojojin Ƙasa ta Libiya (LNA) da ke gabashin ƙasar a karkashin Khalifa Haftar.
Kafin tsagaita wutar, Turkiyya ta riga ta ƙulla muhimmiyar alaƙa da Libya, inda ta sanya hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci ta teku da gwamnatin Tarabulus a shekarar 2019 wadda ta raba yankunan da ke ƙarƙashin ikonta a Gabashin Bahar Rum mai arzikin iskar gas. Bayan tsagaita wutar, Ankara ta ƙara mayar da hankali kan gabashin Libya.
"Tun bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta shekarar 2020, dangantakar Turkiyya da yankin gabashin Libya ta wuce matakin bayar da tallafin jinkai da ayyukan sake gina wurare, inda ta kunshi hadin gwiwa mai zurfi a fannonin siyasa, tattalin arziki, da tsaro," in ji Ferhat Polat, babban mai bincike kuma masani kan harkokin siyasa da tsaron yankin Arewacin Afirka, yayin da yake zantawa da kafar TRT World.
Polat ya bayyana cewa, Saddam Haftar—karamin dan Khalifa Haftar, wanda aka nada a matsayin mataimakin babban kwamandan sojojin gabas a watan Agustan 2025—ya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata wannan dangantaka, inda ya ziyarci Turkiyya sau da dama tare da ganawa da manyan jami'an kasar.
A cewar Polat, ziyarorin da Haftar ya yi, tare da karuwar hulda tsakanin hukumomin Ankara da na gabashin Libya, sun bude sabbin hanyoyin sadarwa tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ke bayar da gudunmawa ga tattaunawar kasa da ake gudanarwa tsakanin gwamnatocin yammaci da gabashin Libya masu adawa da juna.
Ya kuma yi nuni da karuwar karfin tsaron Turkiyya da kuma alakar soja da ke tsakaninta da Libya a matsayin abubuwan da za su iya taimaka wa wannan kasa ta Arewacin Afirka wajen kafa tsarin tsaro guda daya a fadin yankinta mi fadi.
A watan Agustan 2025, jirgin ruwan yakin Turkiyya mai suna TCG Kinaliada ya kai ziyara mai muhimmanci a tashar jiragen ruwa ta Benghazi, inda jami'an sojan Turkiyya da na gabashin Libya suka tattauna kan hadin gwiwa a karkashin manufar "Libya Daya, Soja Daya."
"Da zarar an tabbatar da tsaro sosai a fadin kasar, tsarin samar da kwanciyar hankali mai fadi zai iya ci gaba cikin sauki. A wannan yanayi, sanya cibiyoyin sojan Libya a karkashin tsarin jagoranci guda daya abu ne mai matukar muhimmanci," in ji Polat ga TRT World.
"Turkiyya ta bayar da horo da sauran tallafi domin karfafa kwarewa da karfin cibiyoyin sojin Libya."





















