| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kashe mutum 10 tare da kama 11 a harin 'yanbindiga kan ayarin sojin Ghana
Rundunar sojin Ghana ta yi ƙarin haske game da musayar wuta da aka yi tsakanin wani ayarin dakarunta da wasu 'yanbindiga a kusa kan iyakar ƙasar da Burkina Faso
An kashe mutum 10 tare da kama 11 a harin 'yanbindiga kan ayarin sojin Ghana
TSOHON HOTO: Ba kasafai ake samun labarin kai hari kan sojin ƙasar Ghana ba / Reuters

Rundunar sojin Ghana ta yi ƙarin haske game da musayar wuta da aka yi tsakanin wani ayarin dakarunta da wasu 'yanbindiga a garin Binduri da ke kusa kan iyakar ƙasar da Burkina Faso ranar Litinin.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin da dare ta ce lamarin ya auku ne yayin da ayarin sojin ke yi wa fararen hula 140 rakiya.

“An yi harbi kan ayarin da ya fito daga Bawku zuwa Bolga lamarin da ya kashe fararen-hula uku cikin waɗanda ake yi wa rakiya tare da ji wa ɗaya ciwo,” in ji sanarwar da muƙaddashin daraktan watsa labaran rundunar, Kyaftin Veronica Adzo Arhin, ta sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar kashe bakwai daga cikin maharan yayin da suke ba-ta-kashi.

“Sojojin sun bi mutanen inda ɗaya daga cikinsu ya shiga wani masallaci, amma sun ƙwato wata bindiga mai sarrafa kanta ƙirar G3 da gidajen harsashai biyu da ko wannensu ke da harsasai 20 da kuma ƙarin harsasai 176,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa an kama ƙarin mutane 10 da ake zargi kuma suna taimaka wa jami’ai game da bincike.

“Rundunar sojin Ghana tana so ta yi gargaɗi ga jama’a su kauce wa shishshigi cikin lamuran soji da ma duka jami’an tsaro a lokacin da suke ayyukansu,” in ji sanawar da ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan tare da fatan warkewa da wuri ga waɗanda suka jikkata.