SIYASA
2 minti karatu
Ghana tana alhinin mutuwar matar tsohon shugaban ƙasar, Nana Konadu Agyeman-Rawlings
Mutuwarta ta zo kusan shekaru biyar bayan ta mijinta, marigayi Jerry John Rawlings.
Ghana tana alhinin mutuwar matar tsohon shugaban ƙasar, Nana Konadu Agyeman-Rawlings
Tsohuwar mai ɗakin shugaban Ghana Nana Konadu Agyemang-Rawlings ta rasu tana da shekaru 76 a duniya ranar 22 ga watan Oktoba ta shekarar 2025 / User Upload
24 Oktoba 2025

Gwamnatin Ghana da al’ummar ƙasar na cikin alhinin rasuwar matar tsohon shugaban ƙasar Nana Konadu Agyeman-Rawlings.

Nana Konadu Agyeman-Rawlings wadda aka fi sani da Iron Lady, ranar Alhamis a asibitin Greater Accra Regional Hospital tana da shekaru 76, a cewar sanarwar da Ministan Sadarwa, Felix Kwakye Ofosu ya fitar.

Sanarwar ta miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan Rawlings da sauran al'ummar ƙasar Ghana, inda ta bayyana Nana a matsayin wadda ta taka rawa wajen ci gaban ƙasar.

Mutuwarta ta zo kusan shekaru biyar bayan ta mijinta, marigayi Jerry John Rawlings.

Tuni dai manyan ‘yan siyasa da sauran mutane a ƙasar suna fara alhinin rasuwarta.

Shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahamaya ya jagoranci shiru na girmamawa a fadar gwamnatin ƙasa ta Jubilee House kafin a rantsar da sabbin alƙalai 37 da aka naɗa a manyan kotun ƙasar.

Shugaban ya tabbatar da cewa an sanar da gwamnatin rasuwarta a hukumance kuma a jawabinsa ga jami’ai na fannin shari’a da ‘yan siyasa ya nemi a haɗa kai a girmama matar da zama ‘yar takarar shugaban ƙasa a shekarar 2016.

Tsohon shugaban ƙasa Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana alhininsa game da rasuwar Nana Konadu Agyeman-Rawlings, yana mai bayyana ta a matsayin  “mata mai ƙarfin yarda da sha’awar ƙarfafa wa matan Ghana gwiwa.”

Gidan rediyon Joy FM na ƙasar ya ruwaito cewa ɗaukacin ‘yan Ghana — mata ‘yan kasuwa da manoma da malamai a karkara — sun ji zafin rasuwarta sosai. Suna ganin kansu cikin jajircewar matar da, duk da cewa ta bar fadar shugaban ƙasa, ta ci gaba da takara.

Ta yi wa’adi biyu a matsayin matar shugaban ƙasa — ta yi wani gajeren wa’adi a shekarar 1979 da kuma dogon wa’adi daga shekarar 1981 zuwa shekarar 2001 — inda ta sake fasalin kujerar daga mai uwargida ta zamantakewa kawai zuwa wani muƙami mai ƙarfi da ke tasiri kan siyasa.