CBN ya bai wa 'yan canji a Nijeriya damar sayen dala 150,000 a duk mako daga gwamnati
Matakin na zuwa ne yayin da ake samun ƙarin giɓi tsakanin farashin kasuwar gwamnati da kasuwar bayan fage, wanda ya zarce naira 90 a karon farko cikin shekaru uku.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince ‘yan canji masu lasisi su fara shiga kasuwar canji ta gwamnati (NFEM), inda ya bai wa kowane ɗan canji damar ya sayi kuɗin da ya kai dala 150,000 a kowane mako.
Amincewar ta bankin tana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da CBN ya fitar ranar Talata wadda daraktan fannin cinikayya da canji na bankin, Dr Musa Nakorji ya sanya wa hannu ya kuma tura wa bankuna masu lasisi da ma jama’a baki ɗaya.
Matakin na zuwa yayin da ake samun ƙarin giɓi tsakanin farashin kasuwar gwamnati da kasuwar bayan fage, wanda ya zarce naira 90 a karon farko cikin shekaru uku.
Bayanin da CBN ya yi a sanarwarsa
Sanarwar ta ce an fito da tsarin ne domin ƙara yawan kuɗade a fannin saye da sayarwa na kasuwar kuɗaɗen ƙetare da kuma biyan buƙatu da suka dace da doka na masu amfani da kuɗaɗen.
Babban bankin ya ce dukkan kamfanonin ‘yan canji da ke da lasisi an ba su damar neman kuɗaɗen ƙetare daga kasuwar NFEM ta gwamnati ta hanyar duk wani banki dillali da aka bai wa damar shiga kasuwar ta yadda ake sayar da kuɗin a kasuwa.