| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yansandan Nijeriya sun kama Adeniyi wanda ake zargi da kafa hukumar bogi
Ana sa ran Adeyemi zai fuskanci tuhume-tuhume takwas da suka shafi makirci, ƙarya da kuma bayyana kansa a matsayin shugaban hukumar bogi a fadar shugaban ƙasar.
'Yansandan Nijeriya sun kama Adeniyi wanda ake zargi da kafa hukumar bogi
Prince Adeyemi Adeniyi zai fuskanci tuhume-tuhume takwas da suka shafi makirci, karya da kuma bayyana kansa a matsayin wani.

‘Yansandan Nijeriya sun kama Prince Adeniyi Adeyemi, wanda ya ayyana kansa a matsayin Darakta Janar na Hukumar Tallafawa Zuba Jari ta Ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban Ƙasa, bayan sammacin kama shi da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar kan laifukan da suka shafi zamba.

Jami’an Sashen leken Sirri na Rundunar ‘Yansanda Nijeriya (IRT) ne suka kama Adeyemi a ranar Talata a wani wuri da ya ɓuya a Jihar Osun da ke kudancin ƙasar bayan da ya ƙi bayyana a kotu.

Mai Shari'a Mohammed Umar ne ya bayar da sammacin kama shi bayan ya amince da ƙorafin masu gabatar da ƙara kan shari'ar, mai lamba FHC/ABJ/CR/562/2025, bayan wanda ake tuhuma ya ƙi halartar zaman kotun.

Ana sa ran Adeyemi zai fuskanci tuhume-tuhume takwas da suka shafi makirci, ƙarya da kuma bayyana kansa a matsayin shugaban hukumar bogi a fadar shugaban ƙasar.

Lauyansa, Genesis Francis, ya shaida wa kotun cewa Adeyemi ya ƙaurace wa zaman kotun ne saboda tsoron kula da lafiyarsa kuma ya rubuta wa Shugaba Bola Tinubu wasiƙa game da barazanar da rayuwarsa ke fuskanta.

A cewar lauyan, yana “so ya rayu da lafiyarsa don ya iya kare kansa a kotu.”

A martanin da ya mayar, Alƙali Umar ya ce, "Kotun za ta taimaka masa ya rayu," sannan ya bayar da umarnin a kama shi.

An ɗage shari'ar zuwa ranar 30 ga Satumba, 2026, domin ya gurfanar gaban kotu.

Mataimakin Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar ‘yansandan jihar Osun, Aminu Koji ya tabbatar da kamen, wanda ya ce sashen IRT ne ya gudanar da aikin a Jihar.

"Muna tabbatar da kama Mista Adeniyi Adeyemi ta hannun tawagar Sashen Leƙen Asiri na rundunar ‘yansandan Jihar Osun," kamar yadda Koji ya bayyana a cikin sanarwar da aka fitar.

Haka kuma rahoton bidiyo na gidan talbijin na TVC News ya nuna Adeyemi a hannun 'yansanda.

Ana zargin Adeyemi da wasu mutane biyu da aka bayyana su a matsayin Femi da Anu, waɗanda har yanzu ba a san ko su waye ba, da kafa tare da yin aiki a ƙarƙashin Hukumar Tallafawa Zuba Jari ta Ƙasa da Ƙasa da ake zargi ta bogi ce, a cewar takardun kotu da 'yansanda suka shigar a ranar 27 ga watan Nuwamban 2025.

Fadar Shugaban Kasar Nijeriya ta jaddada cewa babu wata hukumar gwamnati irin wannan da ke ƙarƙashinta.