Wasu da ake zargin ’yanta’addan Boko Haram ne sun kashe aƙalla sojoji 10 tare da raunata wasu aƙalla 20 a wani harin haɗin gwiwa da suka kai sansanin sojoji a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya a wannan makon, kamar yadda majiyoyin soji da mazauna yankin suka bayyana ranar a Alhamis.
Majiyoyin soji biyu sun ce ’yanta’addan sun kai hari sansanin da ke ƙaramar hukumar Guzamala a ranar Talata da daddare, inda suka fatattaki sojojin da ke wurin, suka lalata motocin sojoji tare da cinna wa wasu sassan ƙauyen Mairari da ke kusa da sansanin wuta.
Majiyoyin sun ce fiye da mutane 20 sun ji raunuka a harin, yayin da aka kashe aƙalla fararen-hula biyar da wani mai gadin daji.
Majiyoyin sun nemi a sakaya sunayensu saboda ba su da izinin yin magana da kafafen yaɗa labarai
Kyaftin Mohammed Goni, wanda shi ne mai magana da yawun rundunar soji, bai amsa kiran waya ko saƙonnin neman jin ta bakinsa kan harin ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
Kafin kai hari a sansanin sojojin, ’yanta’addan sun ƙwace kwale-kwalen kamun kifi fiye da 40 a Tumbun Barebari, wani ƙauye da ke bakin tafki a kusa da wurin, in ji Jibrin Hassan, wani masunci da ya rasa kwale-kwalensa a harin.
Babagana Muhammad, wanda shi ma wani masunci ne, ya ce, “harin an kai shi ne a lokaci guda, sai dai bambancin shi ne ba a cutar da mu masunta ba.”
Hare-haren ƙungiyoyin ta’addanci, ciki har da Boko Haram da ISWAP, sun ƙaru a makonnin baya-bayan nan, duk da shekaru ana gudanar da ayyukan soji da nufin shawo kan matsalar rashin tsaro da ta shafe shekara 17 tana addabar arewa maso gabashin Najeriya.
A makon da ya gabata, sojojin Nijeriya sun dakile wani hari da aka kai kan wani sansanin soji a jihar Borno, inda suka kashe ’yanta’addan ISWAP fiye da 25, duk da cewa ba a bayyana adadin sojojin da suka rasa rayukansu a harin ba.



















