Diallo ya taimaka wa Ivory Coast ta ci wasanta na farko a AFCON 2025
Ɗanwasan Manchester United Amad Diallo ya ci wa Ivory Coast ƙwallo ɗaya tilo wacce ta bai wa ƙasar nasara a kan Mozambique a wasan farko da ta buga a wasan rukunin F.
Ivory Coast ta ɓarar da damarmaki masu yawa da ta samu kafin a tafi hutun rabin lokaci ko da yake Diallo ya yi nasarar zura wa Mozambique ƙwallo a raga a minti na 49.
Ɗanwasan Ivory Coast Wilfried Zaha wanda ya buga wa ƙasar wasansa na farko a cikin shekaru biyu, ya ɓarar da damarmaki masu yawa yayin da ɗanwasa Franck Kessie ya zubar da manyan damarmaki guda biyu.
Sakamakon wasan ya sa yanzu Ivory Coast ta zama ita ce ta biyu a rukunin F. Ƙasar ce ta lashe kofin gasar da aka yi a shekarar 2024.
Kamaru ce take jan ragamar rukunin F bayan da ta doke Gabon da ci 1-0.
A rukunin E, Aljeriya ce a kan gaba bayan da ta doke Sudan da ci 3-0.
Riyad Mahrez ya ci ƙwallaye biyu cikin ukun da Aljeriya ta doke Sudan yayin da bayan da aka dawo hutun rabin lokaci Ibrahim Maza ya ciyo wa Aljeriya ƙwallo ta uku a minti na 85.