Yadda duniya ta rungumi shan gahawa kuma manoma a Afirka suke samun alheri
A wani mataki mai cike da tarihi, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ranar 1 ga Oktoba a matsayin Ranar Kofi ta Duniya. Wannan martabawar tana ishara ga al'ummar Afirka da ke noman kofi.
Hasken alfijir yana fitowa kan tsaunukan masu cike da raɓa a yankin Yirgacheffe na Habasha. Sama ta ɗauki launukan ruwan lemu da zinariya. Ga Hailu Gebre, ba da hudowar rana gari ke wayewa ba, yana farawa ne cikin sanyi da ƙamshin ƙaramr gonarsa ta kofi, awanni da dama kafin nan.
Yankan saka yatsunsa yana shafar 'ya'yan kofi masu ja-jaja da suke rataye daga rassan itacen, kowanne ƙwallo ana fatan ya zaman wani silar arziƙi abin nema.
"Kakana ya koya wa mahaifina, shi kuma mahaifina ya koya mi ni: kofi ba wai abin da muke shukawa kawai ba ne; shi ne mu," in ji Hailu, a hirarsa da TRT Afrika.
"Amma tsawon lokaci, duniya tana ganin abin sha na kofi ne kawai a cikin kofi. Mutane ba su san mu a nan ba, ga mu a nan muna damuwa da ruwan sama idan bai zo ba, ko farashin da zai iya sauyawa cikin dare. Gane haka da yanzu aka yi, tamkar duniya ta fara sanin manomin da yake silar samuwar kofin kofi."
Abin da Hailu yake ji a yanzu, yana bayyana irin yanayi da ke yaɗuwa a faɗin yankuna da ake noman kofi a Afirka.
Dubban milamilai daga nan, a tsaunuka masu ciyayi a dutsen Mount Kenya, Wanjiku Mwangi, mai mallakar rumfar soya kofi a Nyeri, ta san wannan halin da ake jin yanzu. Ta gina kasuwancinta bisa waken kofi da ke da ƙarfi da ake samu a yankinta, inda takani yi wahalhalun kasuwanci daga nomawa zuwa kai shi kasuwar duniya.
"Abokan cinikina a Turai da Amurka suna son labarin waken kofi, da kuma ɗanɗano na blackcurrant da citrus," Wanjiku ta bayyana, tana nuni da jakunkuna waken kofi korra a ɗakin aikinta.
"Amma labarin ba ya cika idan ba a haɗa babin gwagwarmaya ba, wato gwagwarmayar neman farashi mai adalci, da samun bayanai, da kuma makoma da ba za ta tilasta wa matasanmu barin gonaki ba. Mu ne tushe, kuma muna buƙatar duniya ta zuba jari a wannan tushe."
Wannan karɓuwa a duniya, wadda miliyoyi kamar Hailu da Wanjiku suka daɗe suna fata, a ƙarshe ta iso a fili kuma cikin karfi. A wani mataki mai cike da tarihi, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana a hukumance ranar 1 ga Oktoba a matsayin Ranar Kofi ta Duniya.
Farashin adalci
Wannan ƙuduri, wanda Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta amince cewa da abin da al'ummomi a faɗin Afirka suka sani tun ƙarnoni: kofi ya fi ƙarfin kayan kasuwa. Shi ginshiƙin al'adu ne, kuma wata al'adar kullum ce, kuma ga mutane da dama, hanyar neman abinci ce da gujewa talauci.
Matakin ya bayyana muhimmancin kofi a tsarin al'adu da zamantakewar al'umma, amma girman tasirinsa na fitowa ne a tasirin tattalin arziƙinsa. Kofi yana haɗa hada-hadar kofi da cimma muradun Ci Gaban Mai Ɗorewa (SDGs) masu muhimmanci: daga kawo ƙarshen talauci (SDG 1), da yunwa (SDG 2), zuwa ba mata iko (SDG 5), da kuma ƙarfafa haɓakar tattalin arziƙi (SDG 8).
Ba a samu wata nahiyar da wannan alaƙa ta fi tsanani ba kamar Afirka, mahaifar nau’in kofi mai suna Coffee Arabica. Duk da cewa manyan ƙasashe kamar Brazil da Vietnam suna gaba a yawan fitarwa, ƙasashen Afirka suna samar da wasu daga cikin nau’i mafi daraja da ingancin a duniya, kuma nan ne cibiyar kasuwar kofi ta musamman.
Habasha, tana da shahararrun nau'ikan waken kofi Yirgacheffe da Sidamo, kuma ita ba mai samarwa kawai ba ce; kofi shi ne jinin rayuwar ƙasar. A shekarar 2024, kofi ya kai kashi mai ban mamaki na 27.9 cikin ɗari na jimillar fitar da kayayyakin kasuwancin Habasha.
A maƙwabciyarta Uganda, wadda aka sani da nau’in waken kofi mai ƙarfi mai suna Robusta, adadin kasuwancin kofi ya kasance kashi 20.1 cikin ɗari. Sai kuma a Burundi, inda ya kai kashi 19.5 cikin ɗari.
Waɗannan ba kawai adadi ne ba: suna wakiltar kuɗin waje ne da ake sayan muhimman kayan shigowa. Gaskiya ne, a Habasha da Uganda, kuɗaɗen da ake samu daga fitar kofin sun zarce jimillar abin da ƙasar ke kashewa wajen shigo da abinci kaɗai, abin da ke nuna rawar da wannan ɓangaren ke takawa wajen tsaron abinci na ƙasa. A Burundi kuwa, ya rufe kusan kashi 20 cikin ɗari na waɗannan kuɗaɗen.
Alƙaluman duniya ma suna da ban mamaki. Masana'antar mai darajar kimanin dala biliyan 200, tana tallafawa rayuwar kimanin manoma miliyan 25 a duniya. A 2024, an haɓaka yawan kofi na duniya zuwa fiye da ton miliyan 11, tare da kasuwancin ƙasa-da-ƙasa na waken kofi kaɗai da aka ƙiyasta kimarsa ta kai dala biliyan 34.
Fiye da abinsha
Amma wannan babbar harkar tattalin arziƙi tana cikin rauni. Canjin yanayi, yawan sauyin farashi, da sauye-sauyen buƙatun kasuwa na manufofin ɗorewa da iya gano tushe, suna haifar da barazana kan wanzuwar ƙanana manoma.
"Kofi ya fi gaban abinsha; kayan kasuwanci ne da ake safarar sa a duk duniya, daga wake har zuwa hidimar haɗa kofi, wanda ke tallafar rayuwar miliyoyin gidajen noma, kuma yake haɗa al'ummomin karkara da kasuwanni a faɗin duniya," in ji Daraktan-Janar na FAO, Qu Dongyu.
"Gane kimar ɓangaren kofi zai ƙara wayar da kai game da muhimmancinsa a fannin zamantakewa da tattalin arziƙi, kuma zai ƙarfafa gudummawarsa wajen kawar da talauci."
FAO ba kawai tana tsayawa kan alamta muhimmancin kofi ba ne. Hukumar tana aiki a zahiri a faɗin Afirka da sauran yankunan da ke samar da kofi don ƙarfafa ɓangaren.
Daga Gabashin Afirka, ana aiwatar da shirye-shirye don gabatar da nau'ukan kofi masu jurewa canjin yanayi da hanyoyin noman dajin gona. A Uganda da wasu wurare, FAO tana haɗin gwiwa da gwamnatoci don ƙirƙirar tsarin bin diddigin, da tabbatar da cewa manoma za su iya samun kasuwannin alfarma waɗanda ke buƙatar hujjar ayyukan da suka dace.
Ta hannun Cibiyar Zuba Jari da Shirin Hannu-da-Hannu, FAO na taimaka wa ƙasashe kamar Habasha su iya fitar da kuɗaɗen da za su ƙarfafa rayuwar manoma, kuma su gina kima ta dogon lokaci.
Ga Wanjiku Mwangi a Kenya, irin wannan tallafi shi ne canjin da za a iya gani wanda dole ne ya biyo bayan ayyana ranar kofi ta duniya.
"Bikin rana guda abu ne mai kyau," ta faɗa tana mai shirya akwatin waken kofi da ta soya wanda za a kai wani kantin kofi a Nairobi. "Yana ba mu dandalin da za mu ba da labarinmu.
Amma yanzu, da tasirin Majalisar Ɗinkin Duniya a bayanta, dole 1 ga Oktoba ya zama rana ta ɗaukar mataki. Ranar da duniya za ta tuna cewa makomar ɗorewar kofi ta fara ne da rayuwa mai ɗorewa ga manomi."
A gonakin Habasha, yayin da rana ke hawa sama kuma hazo ya fara raguwa, Hailu Gebre yana kallon shukokinsa da sabon fata. Zai yi murna a ranar 1 ga Oktoba. Zai yi kyautar kofin kofi mafi kyawun haɗi ga maƙwabtansa. Amma a gare shi, ainihin ma'aunin wannan sabuwar ranar ta duniya za a gani ne bayan an sha kofin kofi na ƙarshe.
"Mun daɗe da sanin kimar aikinmu," in ji Hailu, yana mai muryar alfahari. "Yanzu, duniya ta furta hakan a fili. Fatana shi ne 1 ga Oktoba ba kawai ta zama don murnar kofi ba, amma don murnar hannuwan da suke sanya aikin ya yiwu. Makoma mai kyau ga kofi tana farawa ne da rayuwa mai kyau ga manomi."