Shugaban Nijeriya Tinubu ya sanya hannu a kan sababbin Dokokin Haraji

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokoki huɗu masu muhimmanci da ke da manufar kwaskwarima ga tsarin tattara haraji a ƙasar a ranar Alhamis.

Shugaba Tinubu yayin sanya hannu kan sababbin Dokokin Harajin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja

A yayin wani taro da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Abuja babban birnin Nijeriya a ranar Alhamis, shugaban Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokokin haraji da aka yi wa kwaskwarima, waɗanda a baya suka janyo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.

An ɗauki tsawon lokaci gwamnatin ƙasar mai jihohi 36 na son kwaskwarima ga tsarin tattara haraji a kasar, tana mai cewa sabon tsarin zai daidaita karba da rarraba haraji a fadin kasar.

"Tsawon lokaci, tsarin harajinmu ya kasance wani abu mara tsari mai kyau - mai rikitarwa, wanda babu adalci, da dora nauyi," Tinubu ya bayyana haka a wani sako da ya fitar ta shafukan sada zumunta kafin sanya hannun.

Tinubu ya yi alkawarin samun sauki ga talakawa da masu aiki a Najeriya.

Sauye-sauyen da shugaban kasar ya yi tun da farko sun hada da janye tallafin man fetur mai tsada da kuma sassauta farashin canjin Naira -- ya samu yabo daga masana tattalin arziki da ke cewa an ma makara wajen daukar irin wadannan matakai.

Amma kuma matakan sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a Nijeriya.

Dokokin hudu su ne – Dokar Harajin Najeriya, da Dokar Kula da Ayyukan Harajin Najeriya, da Dokar Kafa Hukumar Tattara Haraji ta Kasa, da Dokar Hukumar Kula da Haraji ta Kasa ta Hadin gwiwa.

Dokokin za su kara yawan kudaden da ake samu a kasar, sanna za kuma su rage nauyin biyan haraji kan masu karamin karfi, in ji wani kwararre kan harkokin haraji Chukuemeka Eze a yayin tattunawa da AFP.

Yayin da kasar ke fuskantar matsalolin tattalin arziki mafi muni cikin shekarun da suka gabata, sabbin dokokin sun kebe kananan ‘yan kasuwa masu karamin karfi daga biyan harajin kamfanoni da kuma rage harajin kamfanoni zuwa kashi 25 cikin dari daga kashi 30 cikin dari.

Gwamnatin ta kuma kawo tsarin bai daya na tattara haraji tare da sauya fasalin rabon kudaden shiga tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi.

An yi watsi da manyan sauye-sauyen tsarin rabon kudaden shiga yayin da kudurorin suka je hannun majalisun dokoki na kasa, bayan da aka fahimci yadda kudu da arewacin aksar suka bambanta da juna ta fuskar arziki, addini da kabila.

Daya daga cikin dokokin sun sauya sunan Hukumar Tattara ta Cikin Gida ta Nijeriya zuwa Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS), inda mahukunta suka ce manufar hakan ita ce karfafa yanayin samun kudaden shiga, duk da cewa kudaden da gwamnatin tarayya ke samu daga harajin (VAT) zai ragu, inda za a ware karin kudade ga daidaikun jihohi.