Saudiyya a ranar Jumma'a ta sanar da kammala hajjin wannan shekarar cikin nasara, ta ce tsarin tsaro, tsari da ayyuka masu haɗaka sun ba mahajjata damar yin ibadunsu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.
Sanarwar ta fito ne daga Yarima Saud bin Mishal bin Abdulaziz, mataimakin gwamnan yankin Makkah da mataimakin shugaban Kwamitin Dindindin na Hajj da Umrah, a wata sanarwa ta talabijin a daren kammala Aikin Hajjina bana.
Yarima Saud ya ce kakar hajjin 2026/1447 AH ta shaida "tsarin tsaro, tsari da ayyuka masu haɗaka" wanda ya ba mahajjata damar aiwatar da ibadunsu cikin natsuwa da aminci.
Yarima Saud ya jaddada cewa nasarar hajji ba ƙarshen aiki ba ce, amma farkon sabbin nauyi ne, inda ya sabunta alkawarin Saudiya a kowace shekara na ci gaba da taka rawa wajen hidimar Musulunci da Musulmai.
A ranar Talata, Hukumar Kasa ta Kididdiga ta Saudiyya ta ce jimillar mahajjata na wannan kakar ta kai 1,707,301, inda mahajjata 1,546,655 suka kasance daga kasashe 165. Sauran mahajjata 160,646 kuma mazauna Saudiyayan ne.
Jimillar adadin ya zarce na bara, wanda ya kai mahajjata 1,673,230 daga cikin gida da wajen masarautar, amma har yanzu bai kai sama da mahajjata miliyan 1.83 da aka samu a shekarar 2024 ba. Ana sa ran Aikin Hajjin bana zai ƙare ranar Asabar.
Ayyukan Hajji a hukumance sun fara ne ranar Litinin da isowar alhazai Mina da ke yammacin Saudiyya, tare da ɗimbin shirye-shiryen hidima da matakan tsaro domin sauƙaƙa gudanar da aikin Hajji.
Lokacin Hajjin na kwanaki shida ya haɗa da tsayuwa a Arafat ranar Talata, kwana a Muzdalifah, jifar shaidan, da kuma ɗawafin bankwana a Masallacin Ka’aba.














