Kusan mutum miliyan 90 da aka tilasta wa barin gidajensu a faɗin duniya ne ke fuskantar haɗurra masu tsanani da suka shafi yanayi, ciki har da fari, ambaliya da matsanancin zafi, kamar yadda Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana ranar Juma’a.
“Hasashe ya nuna cewa ambaliya mai tsanani da ke da alaƙa da yanayin El Niño na iya tilasta wa mutum miliyan uku barin gidajensu a faɗin Somaliya da Kenya da Sudan ta Kudu da Uganda kafin ƙarshen shekarar 2026, gwargwadon tsananin ambaliyar,” kamar yadda wani babban jami’in UNHCR ya bayyana.
Wannan gargaɗi na zuwa ne gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP31, wanda Turkiyya za ta karɓi baƙuncinsa a birnin Antalya daga ranar 9 zuwa 20 ga watan Nuwamban 2026.
A wani rahotonta na baya-bayan nan, UNHCR ta yi gargaɗin cewa kusan mutum uku daga cikin huɗu da aka tilasta wa barin gidajensu a faɗin duniya na zaune ne a ƙasashen da ke fuskantar haɗurra masu nasaba da yanayi.
Matakin gaggawa
Hukumar ta yi kira da a ɗauki “matakin gaggawa” domin kare ’yan gudun hijira da sauran mutanen da suka rasa matsugunansu daga illolin sauyin yanayi da ke ƙara ta’azzara, gabanin taron COP31 da za a gudanar a Antalya, Turkiyya.
“Nan da shekarar 2050, ɗaya daga cikin sansanonin ’yan gudun hijira uku a ƙasashen Afirka kudu da Sahara na iya fuskantar aƙalla kwanaki 100 na zafi mai haɗari a kowace shekara,” in ji hukumar.
“’Yan gudun hijira na fuskantar rashin adalci iri biyu. Bayan an tilasta musu barin muhallansu saboda rikicin da ba su suka haddasa ba, yanzu suna sahun gaba wajen fuskantar bala’in sauyin yanayi, duk da cewa gudummawarsu wajen haddasa shi ba ta taka kara ta karya ba,” in ji Anton Leis Garcia, mataimakin kwamishinan ayyuka na UNHCR.
Leis Garcia ya ce sauyin yanayi ba wani “haɗari ne da ke can nesa” ga miliyoyin mutane ba, domin tuni ya fara lalata hanyoyin samun abincinsu da abin rayuwarsu.
Ya yi gargaɗin cewa duniya “ba za ta iya barin waɗanda suka riga suka yi asarar abubuwa da dama a baya a ƙoƙarin tunkarar sauyin yanayi na duniya ba.”
Barazana ga mafita mai ɗorewa
Rahoton UNHCR ya kuma jaddada cewa sauyin yanayi na barazana ga yiwuwar samar da mafita mai ɗorewa ga mutanen da aka tilasta wa barin gidajensu.
Hukumar ta bayyana cewa fiye da mutum biyu cikin mutane uku na ’yan gudun hijira da suka koma ƙasashensu a farkon rabin shekarar 2026 sun koma ƙasashe ne da ke da matuƙar rauni ga haɗurran da suka shafi yanayi.
UNHCR ta ce bala’o’in da suka shafi yanayi sun tilasta wa mutane fiye da miliyan 255 barin gidajensu a faɗin duniya cikin shekaru goma da suka gabata, wanda ke nufin cewa kusan mutum 70,000 ne ke rasa matsugunansu a kowace rana.
Duk da ƙaruwar waɗannan haɗurra, ƙasashe masu rauni da rikici ya shafa na samun kashi 10 cikin 100 ne kawai na kuɗaɗen da ake warewa a duniya domin tunkarar sauyin yanayi, kamar yadda rahoton ya bayyana.
“Muna buƙatar zuba jari a harkokin sauyin yanayi domin ya isa ga al’ummomin da suka fi buƙatarsa,” in ji Leis Garcia.
“’Yan gudun hijira da al’ummomin da ke karɓar baƙuncinsu dole ne su kasance cikin waɗanda ake ware wa wannan jari tun daga farko, ba a ɗauke su a matsayin waɗanda za a yi tunani a kansu daga baya ba,” in ji shi.
UNHCR ta ce za ta yi kira ga gwamnatoci da hukumomi a taron COP31 da su haɗa ’yan gudun hijira da sauran mutanen da aka tilasta wa barin gidajensu cikin tsare-tsaren tunkarar sauyin yanayi da kuma shirye-shiryen samar da kuɗaɗen aiwatar da su.



















