| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Mutum huɗu sun rasu a hatsarin jirgin ƙasa a jihar Delta ta Nijeriya
Hatsarin na ranar Litinin ya zo ne watanni bayan wani hatsarin sauka daga layi a Nuwamban 2025, wanda aka ɗora alhakinsa kan ayyuka masu ɓarnata kayayyakin sufuri.
Mutum huɗu sun rasu a hatsarin jirgin ƙasa a jihar Delta ta Nijeriya
Hadarin jirgin ƙasa / Reuters

Ma’aikatar Sufuri ta Nijeriya ta sanar da rasuwar mutane huɗu, ciki har da jariri guda a wani hatsarin jirgin ƙasa da ya sauka daga layin dogo a garin Agbor na jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Wata sanarwa daga babban sakataren ma’aikatar sufurin, Funsho Adebiyi, ta ce jirgin na ɗauke da mutum 420 lokacin da hatsarin ya abku ranar Litinin 8 ga Afrilun 2026.

Sanarwar ta ce, “Rahotannin farko-farko sun nuna cewa tarago huɗu ne suka kife yayin da tarago ɗaya ya sauka daga layi, abin da ya haddasa mummunan lamarin rasuwar rayuwa huɗu, ciki har da fasinjoji mata manya biyu, namiji babba ɗaya, da jariri ɗaya.”

“Jimillar fasinjojin 442 ne suka hau jirgin, sai ma’aikatan jirgi su 40, da jami’an tsaro, da kuma wasu ma’aikatan daban masu tallafawa aiki, wanda ya kawo jimillar mutane 482 cikin jirgin.”

Ɓarnata kayayyakin sufuri

Adebiyi ya bayyana cewa an kammala ayyukan ceto da kusan ƙarfe 6:30 na yamma, inda aka kai waɗanda suka jikkata zuwa cibiyoyin lafiya a Agbor don samun magani. Ya kuma tabbata da cewa cikinsu akwai mutum 24 masu “matsanaincin raunuka.

Haka nan, Hukumar Jirgin Ƙasa ta Nijeriya, (NRC) ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu tare da addu’ar neman lafiya ga waɗanda suka samu raunuka”.

Hatsarin na ranar Litinin ya zo ne watanni bayan wani hatsarin sauka daga layi a Nuwamban 2025, wanda aka ɗora alhakinsa kan ayyuka masu ɓarnata kayayyakin sufuri.

A Nuwamban, hukumar NRC ta ce ta kama mutum biyu dangane da hatsarin jirgin da ya faru a layin dogo na Warri-Itakpe a Agbor, Delta State.

Haka ma a Agustan 2025, wani jirgin fasinja da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layi, wanda ya haddasa ruɗani a zukatan fasinjoji da danginsu.