WASANNI
1 minti karatu
Griezmann ya zama ɗan wasan Atletico Madrid na farko da ya ci ƙwallo 200
Kocin Atletico Madrid, Diego Simeone ya jinjina wa ɗan wasan gabansa, Antoine Griezmann kan cin ƙwallaye 200 da ya yi wa kulob ɗin.
Griezmann ya zama ɗan wasan Atletico Madrid na farko da ya ci ƙwallo 200
Griezmann ya cim mam wannan mataki ne a wasan Atletico Madrid da Eintracht Frankfurt a gasar Zakarun Turai.
1 Oktoba 2025

Tauraron ɗan wasan Atletico Madrid ta Sifaniya, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ciyo mata ƙwallaye 200.

Ranar Talatan nan ne ɗan wasan ɗan asalin Faransa ya ɗauki wannan kambi yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1.

Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru."

Mai shekaru 34, Griezmann ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan matsayi.

Jinjina daga koci

Simeone ya ce "Ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya ci ƙwallo 200, wanda abin al’ajabi ne.”

A ƙarshen kakar bara, an yi ta raɗe-raɗin Antoine Griezmann zai bar ƙungiyar, amma sai ya tsawaita kwantiraginsa zuwa 2027.

Sai dai a kakar bana, mintuna 416 kawai ya buga zuwa yanzu a wasanni tara, inda yake yawan shigowa wasa daga benci.

A halin yanzu, a kakar bana ana hasashen Griezmann zai zama ɗan Atletico na huɗu da ya buga mata wasanni 500, baya ga Adelardo, da Koke, da kuma Jan Oblak.