Trump ya ce Amurka za ta bar Iran cikin makonni 2 zuwa 3

Shugaban Amurka ya yi iƙirarin cewa tuni aka fara cim ma burin hana Iran mallakar makamin nukiliya ta hanyar matakin soji.

By
Trump na nuna cewa hare-haren kan Iran sun kusa zuwa ƙarshe. / AP

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dakarun ƙasarsa za su bar yaƙin Iran cikin "makonni biyu zuwa uku," inda yake nuna kawo ƙarshen hare-haren da ake kaiwa ƙasar.

"Abin da zan yi kawai shi ne na bar Iran, kuma za mu yi hakan nan ba da jimawa ba," kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai a Fadar White House.

"Za mu bar wurin nan ba da jimawa ba," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa hakan zai iya faruwa “cikin makonni biyu ko uku."

Ya ce an riga an cim ma burin gwamnatinsa na hana Iran mallakar makamin nukiliya.

"Ba za su samu makamin nukiliya ba. Kuma an riga an cim ma wannan burin," in ji shi.

Trump ya kuma ce hare-haren Amurka sun raunata ikon sojin Iran sosai, yana mai iƙirarin cewa Tehran za ta shafe “shekaru 15 zuwa 20” kafin ta iya sake gina ƙarfin sojinta.

"Za mu bar (ƙasar) nan ba da jimawa ba, kuma idan Faransa ko wasu ƙasashe na son samun mai ko gas, za su bi ta Mashigar ruwan (Hormuz)," in ji shi.

"Za su iya biya wa kansu buƙata. Ina ganin zai kasance wuri mai aminci, amma babu ruwanmu da wannan."

Amurka da Isra’ila sun yi ta kai hare-hare kan Iran tun ranar 28 ga watan Fabrairu, inda suka kashe fiye da mutum 1,340, in ji hukumomin Iran.

Iran ta mayar da martani da hare-haren jirage mara matuƙa da makamai masu linzami kan Isra’ila da Jordan da Iraƙi da ƙasashen Larabawa na gaɓar teku da ke da sansanonin sojin Amurka.

Aƙalla jami’an sojin Amurka 13 ne aka kashe tun lokacin da yaƙin ya ɓarke, in ji bayanai na hukuma.

Rikicin ya tayar da farashin makamashi tare da katse jigilar kayayyaki ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar mai ta duniya inda kashi 20 na mai da duniya ke amfani da shi ke wucewa.