Iran ta ce lokaci ya yi da Saudiyya za ta kori sojojin Amurka daga yankinta
Babban jami'in diflomasiyyar Iran Abbas Araghchi ya buƙaci Saudiyya da ta kori sojojin Amurka a yankinta bayan harin da aka kai wa wani kamfanin jiragen sama na Amurka a kasar.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya buƙaci Saudiyya da ta kori sojojin Amurka daga yankinta, yana mai jaddada cewa hare-haren da take kai wa yankin sun shafi abokan gabanta ne kawai.
"Iran tana girmama Masarautar Saudiyya kuma tana daukarta a matsayin 'yar’uwarta," kamar yadda Ministan Harkokin Waje Iran Abbas Araghchi ya wallafa a shafin X.
"Ayyukanmu na kai hari, muna yin su ne kan abokan gaba wadanda ba sa girmama Larabawa ko Iraniyawa, kuma ba za su iya samar da wani tsaro ba... Kalli abin da muka yi wa rundunar sojin samansu. Lokaci ya yi da za a kori sojojin Amurka."
Kalaman nasa sun biyo bayan lalata wani jirgin sama mai saukar ungulu da kuma tsarin sarrafa jiragen a wani harin da Iran ta kai kan sansanin sojojin Amurka a Saudiyya.
Hotuna sun nuna yadda aka lalata mafi yawan ɓangaren bayan jirgin saman E-3 Sentry a sansanin sojojin sama na Yarima Sultan, mai nisan kilomita 128 kudu maso gabashin Riyadh.
Kazalika an ji wa wasu sojojin Amurka da dama rauni a harin na ranar Jumma'a, kuma akalla jirgin sama ɗaya ya lalace, kama yadda wanu jami'an Amurka ya tabbatar.