‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?

Ikirarin Trump na “kisan kiyashi ga Kiristoci” a Nijeriya na jirgita gaskiyar rikici mai rikitarwa da albarkatun kasa ke janyo wa, kuma matakin na da hatsarin ware abokiyar yaki da ta’addanci, da bayyana diflomasiyyar kudi ta gwamnatinsa.

By
Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta musanta kalamin na Trump da ke cewa ana aikta kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya.

Lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafin sadarwa na Truth cewa yana umurtar Pentagon da ta shirya kai hare-haren soji kan Nijeriya, jami'ai a Abuja sun yi mamaki.

Zargin na Trump: Kasar da ta fi yawan jama'a a Afirka ta ba da damar a yi "kisan kare dangi" ga Kiristoci.

Ikirarin, wanda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi watsi da shi nan take a matsayin ba gaskiya ba, ya haifar da wata mummunar tarzoma ta diflomasiyya wadda ta kara ta'azzara cikin sauri yayin da Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin "Kasar da ke da damuwa ta musamman" kan zargin take 'yancin yin addini.

Tuhumar gwamnatin Trump ta yi daidai da matsin lamba daga kungiyoyin bishara na Amurka da wasu 'yan majalisa, wadanda suka dade suna matsa lamba kan jami'an Najeriya da suke zargi da ba da damar "kisan kiyashi ga Kiristoci".

To, menene 'Gaskiya' kan kalamin na Trump?

Yawan al'ummar Najeriya miliyan 220 ya rabu kusan kunnen doki tsakanin Kiristoci da Musulmi, inda na biyun ya fi yawa a arewa, na farkon kuma ya fi yawa a kudu.

Jirkita gaskiyar lamarin

Najeriya ta daɗe tana fama da rikicin masu dauke da makamai a yankunan tsakiya da arewa.

Sojoji na fafatawa da ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ƙungiyoyin 'yan fashi a arewa maso gabas da arewa maso yamma, dukkan yankunan da galibin mazaunansu Musulmai ne.

Wannan yana nufin cewa Musulmai galibi su ne waɗanda wannan ɓarna ta fi shafa.

Trump bai fayyace irin kisan da yake nufi ba, amma ikirarinsa na "kisan kare dangi ga Kirista" ya ta'allaka ne akan rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a tsakiyar Najeriya.

Masu sharhi kan tsaro sun ce tashin hankalin da ke faruwa a yankunan ya ta'allaka ne da samun albarkatun kasa. Kiristoci da Musulmai duka suna faɗa wa cikin irin wannan rikici ba tare da bambancewa ba.

Albarkatun da ake magana sun haɗa da wuraren kiwo da ma'adanai masu mahimmanci kamar lithium da zinare.

Kokarin mayar da martani

Kalamin na Trump na raina wata matsala mai sarkakiya ta tsaro kuma yana iya ƙara ta'azzara rarrabuwar kawuna da rashin zaman lafiya a Najeriya, in ji masana yayin da suke gargadi.

'Yan Nijeriya a duk gidajen siyasa sun yarda cewa Trump bai yi daidai ba a tsarinsa, wanda hakan zai iya haifar da rashin nasara ga kowa, a cewar waɗanda suka yi magana da TRT Afrika.

Barazanar da Shugaban Amurka ya yi na daukar matakin soja a kan Nijeriya, wadda ya yi ba tare da tunanin me zai je ya komo ba, wanda yana kuma da hatsarin ware gwamnatinsa daga kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, kuma babbar kawa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

"Gwargwadon yadda muke yada wadannan labaran, gwargwadon yadda muke taka rawa a hannun 'yan ta'adda, kuma Amurka da kawayenta za su raba kan 'yan Nijeriya.

A karshe, ba za su rasa abokan hulda da za su yaki ta'addanci tare da su ba," in ji Bulama Bukarti, wani mai sharhi kan harkokin siyasa na Najeriya, yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Sake jaddada wanzuwar kalubale

Bayan barazanar Trump, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar yin aiki tare da abokan hulɗa don magance matsalar tsaro a kasar.

Amma kwararru sun ce akwai yiwuwar gwamnati ta fuskanci mummunan yanayi na tashin hankali da ya haifar da barna a cikin shekaru ashirin da suka gabata.

Sojojin kasar sun bazu a wurare da dama da ake rikici - suna yaƙi da Boko Haram a arewa maso gabas, ƙungiyoyi masu alaƙa da Al Qaeda a arewa maso yamma, da kuma 'yan fashi a yankin tsakiya.

Ƙarfin sojojin Nijeriya bai ƙaru ba idan aka kwatanta da ƙalubalen tsaro saboda rashin kuɗi, yayin da adadin jami'an 'yan sanda ya bazu a ko’ina faɗin ƙasar.

"Sojojin Nijeriya har yanzu ba su da kayan aiki. Ba su da kayan aikin da suke bukata, gami da makamai da ƙwarewar leƙen asiri," in ji Bukarti.

"Akwai ƙarancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi a ƙasar da ke da hukumomin tsaro da na tabbatar da aiki da doka da oda sama da 17, waɗanda duk suna da rawar da za su taka wajen dawo da tsaron."

Kaucewa fada wa kangin wahala

Kasancewar Nijeriya a matsayin "Ƙasar da ke da damuwa ta musamman" babban koma baya ne ga Nijeriya, kuma sakamakon zai iya zama mummuna a ƙasar da ta fuskanci mummunan rikicin tattalin arziki a cikin shekaru da dama.

Masana sun ce tabbatar da alaƙar Najeriya da gwamnatin Trump a kan hanya mai kyau zai buƙaci Abuja ta ɗauki matakai na gaske don gyara katangar diflomasiyya da ke tsakaninta da Washington.

"Na farko shi ne gwamnatin Najeriya ta bi a sannu, kar ta fuskanci Trump kamar yadda Trump ke kusantar mu. Gwamnatin Najeriya ba za ta iya biyan Trump ko da da kuɗinsa ne," in ji Bukarti.

"Ya fi kyau a ce su yi hulɗa ta diflomasiyya tare da nuna cewa duk 'yan Nijeriya suna fama da tashin hankalin kuma su yi aiki tare da Amurka ta hanyar da ta dace don ganin ko akwai hanyoyin da za su iya tallafa mana ta fuskar makamai, horo da kuma leƙen asiri."

Tun daga lokacin, mai magana da yawun shugaban ƙasar Nijeriya ya nuna cewa ikirarin Trump "rashin sadarwa ta kwarai ne", yana fatan shugabannin ƙasashen biyu za su "warware" bambance-bambancensu.

Manufar a ni in ba ka ta Trump

Gwamnatin Trump ta yi yarjejeniya da wasu ƙasashen Afirka don karɓar 'yan gudun hijira ‘yan wasu ƙasashen, a wani bangare na yaƙin da gwamnatin ke yi da bakin haure marasa takardun zama a Amurka.

Ghana, Eswatini, Rwanda da Sudan ta Kudu sun karɓi irin waɗannan 'yan gudun hijirar. Uganda ta amince da wata yarjejeniya amma har yanzu ba ta karɓi ko ɗaya ba.

Najeriya ta ƙi shiga cikin shirin korar 'yan gudun hijirar, kuma ƙwararru sun danganta wannan shawarar da janyo rashin jituwa da gwamnatin Trump.

Masana sun ce an kirkiri hanyar kulla mu’amala ta Trump ne don matsa wa shugabanni lamba da kuma cire musu sassauci, wata dabara da ya yi amfani da ita kwanan nan a kan Afirka ta Kudu da iƙirarin kisan kare dangi na fararen fata - wanda Pretoria ta musanta tare da cewa hakan ba daidai ba ne.