An daɗe ana kallon maza musamman matasa a matsayin waɗanda suka fi faɗawa cikin halayyar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Amma yanzu, wata sabuwar barazana na ƙara bayyana a wasu jihohi kamar Jihar Kano.
Mata ciki har da matan aure, da mata masu shekarun suna ƙara shiga ta’ammuli da kwayoyi. Kuma masana na gargadin cewa idan uwa ta lalace, iyali da al'umma baki ɗaya na iya fuskantar mummunan sakamako.
Me ya jawo wannan matsala? Kuma wane haɗari take haifarwa ga iyali da makomar al'umma?
