| Hausa
Yadda batun Falasdinu ya sa Musulmai suka goyi bayan Sifaniya a karawa da Aegentina
Yadda batun Falasdinu ya sa Musulmai suka goyi bayan Sifaniya a karawa da Aegentina
A cikin wannan bidiyon mun yi duba kan yadda batun Falasɗinu da Isra'ila ya yi tasiri wajen sa ƙasashen Musulmai suka goyi bayan Sifaniya a wasan na ƙarshe.

Nasarar da Sifaniya ta samu a kan Argentina da ci 1-0 a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta fito da yadda siyasa da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya suka jawo wa ƙasar Argentina bakin jini a kokarin ƙasar na sake cin babban kofin a karo na huɗu a tarihi.

Tun gabanin wasan wanda aka buga a ƙarshen mako, kan wasu daga cikin masu sha’awar ƙwallon ƙafa a duniya ya rabu biyu yayin da wasu suke goyon bayan Argentina, wasu suna goyon bayan kasar Sifaniya ne.

Ƙarin Bidiyoyi
Ankara da Istanbul: Mene ne bambancinsu?
Makudan kudin fansa da masu garkuwa da mutane ke samu a Nijeriya
Jama'a sun yi dashen shinkafa don nuna rashin amincewa kan jinkirin aikin hanya
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abubuwan da za su iya yin illa ga lafiya
Ko kun san cewa talauci yana rage kaifin basira?
Me ya sa manyan maza suke kuka saboda kwallon kafa?
Me harin Saudiyya da Amurka a Iraki ke nufi?
Me ya sa daukar cikin 'yan mata masu shekaru 15-19 ya zama abin damuwa a Ghana?
Kasar da ake cin tarar wadanda ba su fita kada kuri'a ba
Kasashen Afirka 10 da suka fi yawan mutanen da suka mallaki dala miliyan daya