| Hausa
Nijeriya na fuskantar tsadar fetur duk da matatar Dangote na aiki da cikakken karfin ta
00:39
Nijeriya na fuskantar tsadar fetur duk da matatar Dangote na aiki da cikakken karfin ta
Nijeriya ta samu tashin man fetur mafi girma a cikin ƙasashen Afirka masu ƙarfin tattalin arziƙi bayan girgizar kasuwar mai da ta samo asali daga rikicin Iran.
31 Maris 2026

Tsarin barin kasuwa ta yi halinta a ɓangaren man fetur na Nijeriya ya sa farashin na fetur na tafiya daidai da yadda mai yake a kasuwar duniya duk da matatar Dangote na aiki da ƙarfinta.

Farashin fetur ya ƙaru da fiye da kashi 60 cikin 100 a watan Maris kaɗai, wanda shi ne mafi girman ƙaruwa a cikin manyan ƙasashen Afirka.

Matatar Dangote, mafi girma a Afirka, na aiki da cikakken ƙarfinta na gangar mai 650,000 a rana, tare da ƙaruwa a yawan man da take samarwa kasuwar cikin gida tun daga watan Maris, duk da cewa tana ci gaba da faɗaɗa fitar da mai zuwa sauran ƙasashen Afirka inda a halin yanzu take fitar da kusan gangar mai 214,000 a rana.

Da yake bayani kan hauhawar farashin, Manajan Daraktan matatar Dangote, David Bird ya ce kamfanin na samun kusan jiragen ɗanyen mai guda biyar ne kawai a wata daga cikin gida, wanda ya yi ƙasa sosai da guda 13 zuwa 15 da ake buƙata.

Ƙarin Bidiyoyi
Atiku Abubakar ya ziyarci Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja
Yadda a-daidaita-sahu na 'mata zalla' ke sauya sufuri a birnin Kano
'Yansandan Isra'ila sun far wa yahudawa masu zanga-zangar adawa da hukuncin kisa
Turkawa na murnar sake komawa gasar cin kofin duniya bayan shekara 24
Isra'ilawa sun yi gudun neman mafaka a Haifa
Makami mai linzami na Iran ya sauka a kusa da dakarun Amurka a yankin Gulf
Motoci da yawa sun kone a Isra'ila bayan Iran ta kai hari da bam mai 'ya'ya
TRT Afirka ta cika shekara 3
An yi gagarumar zanga-zanga a fadin duniya don adawa da yakin Amurka-Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
Yadda dubban mutane suka taru yayin da Kwankwaso ya yi rejistar shiga jam'iyyar ADC